Sunday, 7 February 2016

YARE NA YA FIYE MIN WANI YARE CEN

YARENA YA FIYE MIN YAREN WASU CEN DABAN
*********
Mala Ahja Ta ta'ba tambaya ta akan cewa Me yasa na ke son yin rubutu da Yare na, maimakon in rika yi da turanci kowa ma ya fahimta har wayanda ba 'yan yare na ba.

Ban bata amsa ba kawai cewa nayi "HUMMM". Kawai yare na na burgenine.

Nusaiba  'yar yaya ta ce shekarun ta 7 da haihuwa. Wata rana mamarsu ta gargade Nusaiba da yayyenta kada taji wani daga cikinsu yayi yaren Hausa duk wanda yayi zai bada tara.

Haka kuwa akayi saboda Biyayyar yaran dukkansu suka daina hausa suka rika yin turanci.

Ana haka kawai sai ga almajiri ya shigo gidan yana rokon a taimake shi da abinci duk yanda yake yunwa yake ji.

Mahaifiyar Nusaiba ta ce, Nusaiba je kice wa almajiri yayi hakuri yanzu muka dawo daga cikin gari. Wannan maganar da harshen turanci mahaifiyar Nusaiba ta yi mata ita.

Nusaiba cikin ladabi taje har gurin almajiri tace, "PLEASE MY MOTHER SAY I SHOULL TALL YOU WE DO'NT HAVE FOOD...." kafin Nusaiba ta gama bayanin ta nan take wannan Almajirin ya mika mata kwanonsa (a tunaninsa abincin zata bashi).

Babu shakkah wannan abin ya fahimtar dani dalilin da yasa nake rubutu da Hausa.

Babban dalilina shine ina cikin hausawa kuma ina son in habaka yaren nawa ina kuma bukatar wani yare yaji sha'awar yarena.

Hakika da ace da hausa Nusaiba ta fada wa wannan almajirin zai fahimta, amma da yake bada yarensa ta yi masa bayani ba sai ya kasa fahimta.

A cen da Kusan duk wani ilimi na kimiyya ko fasaha ko kuma na ci gaban al’umm a Larabce yake, kuma dole ta sa Turawa
suka yi amfani da nakaltar Larabci don cin moriyar ilimin da ke kumshe a cikin littattafan Larabawa da ke mulkin duniya a wancan lokaci.

Daga baya ne Turawa suka fahimci cewa ai yawancin ilimin da Larabawa ke takama da shi su ma sun kwaso wasu ne daga littattafan Girkawa, don haka suka yi watsi da na Larabawa suka koma wa na ainihin, ta haka ne mallakar da Larabawa suka yi wa duniya ta subuce ta koma ga Turawa, musamman na Ingila.

Ni dai na kasance ina yin rubutu na badan kowa ba sai dan mutanen mu Hausawa kuma ina so su fahimta da kyau.

Rokona gareku yan uwa kai ma in dai har da malam Bahaushe kake magana ko kuma rubutu, to ya dace rubutun nan naka ya kasance a cikin hasrshen da mutanenka za su gane, za su fahimta, za su kuma yi aiki da shi.

Ina Rokon Allah ya daukaka Musulunci da Yaren Hausa.

Jamilu Sani RARAH

No comments:

Post a Comment