Sunday, 12 August 2018

SIHIRIN DA AKAYIWA ANNABI (SAWW)

A madina lokacin da yake Saura Shekaru 4  Annabi (Saww) Ya Kaura ya bar Duniya Al-amarin ya faru.

Sahabban Annabi (Saww) mutum uku suka rawaito Yadda wannan Al'amarin ya faru daga ciki akwai Nana Aisha (RTa) da Abdullahi bn Abbas (RTA) da kuma Zaidu bn Arqam (RTA).

Dukkanin Wayannan sun bada labari cewa, A watan muharram yahudawan madina, (Wato maqiya Annabi (Saww) suka hadu sukayi Wata tattaunawa (meeting) ta sirri sukayi kancewa Annabi Muhammad (Saww) fa addinin shi na karbuwa ko Ina da ko ina, Kuma gashi a baya munyi sihiri kala-kala ya shanye, munyi tsafi don kashi shi bai mutu ba.

Gashi Anyi yaqin badar bai mutu ba, anyi yaqin uhud ma bai mutu ba, Mun shirya makaqarkashiya anyi yaqin kandab amma ya tsira bai mutu ba.

A Duba bayanin Wannan Zama a Cikin Adh-dabaqatul kubra na ibn Sa'ad.

A Wannan Zaman sai sukayi matsaya akan cewa zasu je wajen wani kwararren masihirci a garin madina Mai suna LABIDU BN A'ASAM (Shi wannan Labidu balarabe ne ba yadudu bane), Ya musulunta amma musuluncin Sa na kafircine.

Bayan Sunje Sun Sami Labidu Sai suka ce yayi musu sihirin Da zai kashe Annabi (Saww) zasu bashi dukiya me yawa (dukiya Mai Nishi), suka shirya suka dauki sule uku 3 suka bashi a lokacin sule 3 kudine masu yawan gaske.

Sai Shi wannan masihirci ya nemi akawo Masa Kayan Da zai hada yayi wannan Sihiri dashi da Farko a kawo Masa tokar Zuma (Bayan an tsotse Zuma Akwai Wata tuka tuka), Sannan A Samo Masa tsarkiya kwaya guda (Wani zare Mai Kama da Jijiya Wanda ake yin jita dashi), sannan aje a Samo Masa hudar dabino namiji da Macce, Sannan a Samo Masa Allura guda Goma Sha daya, Abu na karshe Yana so a Samo Masa gashin kan Annabi (Saww).

Duk aka Samo Masa Wayannan Abubuwan Sai Gashin Annabi (Saww) Ne keda Wuya Sai aka samu Wata yarinya ko Yaro wanda yake shiga gidan Annabi (Saww) aka bukaci ta dauko matajin kan Annabi (Saww).

To da aka Sanya wannan yaro ko Yarinya ya dauko matajin Annabi (Saww) wanda yake taje kanshi, Bayan dauko matajin kai na annabi wanda ya tsufa Annabi (Saww) ya dena ma amfani dashi.

Akwai sauran dangashi daya makale jikin matajin, Da wannan gashi masihircin yasamu ya yiwa Annabi (Saww) sihiri dashi. Wannan matsafi Ya tara duk yaranshi mata suka yi ta yin tofi cikin kulli Da tsafe tsafe, daga cikin yayan nashi wata tace lallai indai har Annabin gaskiya ne To Zai bada labarin wannan sihiri Da aka Yi masa, ta fadi haka ne saboda yadda taga karfin sihirin domin sihirine Me hallaka mutum kai tsaye.

Wannan Masihircin yayi mutum mutumin Annabi (Saww) wato yayi gunkinsa Da danko, sai ya sanya gashin da aka samo na Annabi akan kayin gunkin Annabin da yayi. Yayi duk abinda zaiyi ya gama sihiri akaje can bayan gari ya samu wata tsohuwar rijiya wanda aka dena amafani Da ita, yasa aka shiga cikin rijiyar akwai wani duste cikin rijiyar Qato, aka daga wannan dutsen Akasa sihirin kasar aka danne da wannan dutsin.

To Bayan wannan Sai Annabi (Saww) ya fara rashin lafiya gashin kansa Yana zuba Haka kuma baya iya cin abinci sosai, saboda wannan Sihirin har sai da ta kaiga Annabi (Saww) yana ganin ya kwanta Da iyalinshi amma kuma ba haka bane.

Da ciwo yayi tsanani abu na na cigaba yana ramewa, sai Annabi (Saww) yayi ta addu'a yana addu'a yana neman Allah ya ya ye masa wannan ciwo.

Wata Rana Ya kwanta bacci sai yayi mafarkin mala'ika Jibril Da Mika'il su kazo daya ya zauna ta gefen damarsa daya ta gefen hagunsa sai suka Fara hira

mala'ika Mika'il Yace: Me yasamu wannan bawan Allah wato yana tambayar Jibri (AS), Sai Shi Kuma Yace Masa, Ai Anyi masa sihiri ne, sai Mika'il ya Kara tambayawa Cewa, Wayayi Masa sihirin? Sai Mala'ika Jibril Ya fadi Cewa, Labidu ne Dan A'asam, Kuma an binne sihirin ne akarkashin wata riji sunanta BI'IRI ZARWAN ( ﺏﺀﺭ ﺯﺭﻭﺍﻥ ) tana ciki Garin madina.

Wato kamar suna hirane shi kuma Annabi (Saww) yana jinsu. Suka gama suka tafi Sai Annabi (Saww) ya farka yaiwa Allah godiya, yace wa nana Aisha Allah yabani labarin abinda ke damuna kinji kinji wanene yamin sihiri ya binne a rijiya.

Nan take Anabi (Saww) Ya tura sahabbai suje wannan rijiya sukaje suka ya she rijiyar suka shiga suka daga dutsen da ya danne sihirin.

Suka ciro suka bawa Annabi (Saww) da Annabi (Saww) Yaga irin kulle kullen da ke jikin wannan mutum mutumin nashi, yaga ma sihircin ya soka Allurai goma sha dayane 11, a jikin dankon mutum mutumin.

Sai Allah ya saukarwa Annabi Da surori guda biyu wato suratul FALAQI DA NASI.

Idan Annabi (Saww) ya karanta aya daya daga suratul falaqi sai ya zare allura daya daga jikin wannan mutum mutumin nashi, sai yaji kamar ajikinsa aka cire.

Sai da Annabi (Saww) ya karanta surorin nan Masu dauke Da ayoyi goma sha daya ko wace aya in ya karanta sai ya cire allura daya har sai da yaji jikinshi ya warke yasamu lafiya.

A Duba A Cikin Sahihul bukhari Hadisi na 5763-66 har zuwa Da sittin Da shida.

Da sahihu Muslim hadisi na 2189.

Akwai Abubuwan Lura da Yawa a Cikin Wannan Hadisin Wanda ya kamata mu Yi la'akari dasu.

(1) Wannan Yana Nuna Mu'ujizar Annabi (Saww), Ga yadda aka Bayyana Sihirine Mai Girman Gaske Mai saurin Halakarwa. Amma Kuma Bai kashe Annabi (Saww) Ba.

(2) Na biyu Hadin Kai

Duk wani Abu duniya da kuke so ku aiwatar na Alkherine Kona Mugunta Sai Kun hada Kai kamar Yadda wayannan Yahudawa suka hadakansu suka tattauna.

Haka Shima Labid Sai da Taimakon 'Ya'yansa da suka hada Kai Suka You wannan mugun aiki.

(3) Na Ukku da Makusancinka Ake Hadawa Domin Ganin Bayanka.

(4) Tasirin Addu'ah Ga Dukkan wani Lamari da ya tsananta gareka.

Jamilu Sani Rarah Sokoto

Sun 12-08-2018

Saturday, 23 December 2017

AMFANI DA KANYA A MATSAYIN MAGANI BOKANCINE

AMFANI DA KANYA A MATSAYIN MAGANI BOKANCINE
********
Kwanannan Naje Qauye domin ziyara sai na taradda wani al'amari mai ban takaici wanda kusan tun daga wannan rana kullum sai na rika tunani akan wannan al'amari.


Al'amarin shine Wani audio ne ake yawo dashi, wanda wani Mutum ke bayanin Abubuwan da zasu faru a wannan shekara, Inda yace, An aiko shine Daga Saudiya, Kuma duka-duka su Ukku kawai aka aiko a duniya, sannan yace, Wannan shekarar bala’o’I da yawa zasu faru ma’ana shekara ce ta BALA’I, Sannan wannan mutumen yaci gaba da cewa, Duk wanda yasan yana yin bacci tun daga dare har safiya ta waye, to ya daina Idan bai daina ba to kuwa zai mutu matsiyaci a wannan duniya.

Wannan Mutumen ya fadi abubuwa da yawa wanda lokaci ba zai iya barni na kawo suba, Daga karshe dai ya bada magani, Inda yace, A nemi Kanya tana maganin cutukka da yawa a ciki kuwa hard a Ciwon HIV inda yayi rantsuwa cewa, Idan bata maganin HIV Allah Ubangiji yasa HIV ya zama ajalinsa (Iyazan Billahi Iyazah).

Farko dai Wannan Mutumen yayiwa Allah (swt) Qarya, Domin Cewa da yayi wannan shekara ta bala’ice to yana karyata fadin Allah (swt) ne a cikin Alqur’ani Mai girma.

Domin Al-Imamul Bukhaari ya ruwaito hadisi daga Saalim bn Abdullahi, bn Umar, daga Baban Saalim din, wato ( Abdullahi dan Umar(RA)), Yace, Manzon Allah (Saww) yace: “Mabudan Gaibu guda 5 ne, kuma babu wanda yasansu sai Allah (Swt). Sune Allah ya dunqule su a qarshen Suratu Luqman, inda yace: “Lallai ILIMIN TASHIN QIYAAMAH yana wajen Allah ne, kuma shike SAUKAR DA RUWAN SAMA, kuma YASAN ABINDA KE CIKIN MAHAIFA, kuma RAI BATASAN ME ZATA SAMUBA GOBE, KUMA WATA RAI BATASAN A WACE QASACE ZATA MACE BA, lallai Allah masanine mai bada labara” Imamu Bukhari ya ruwaito a hadithi na 4627, a babin tafsiri.

Kenan Cewa, da wannan mutum yayi, Bala’I zai faru a wayannan shekaru kamar yana cewa ne yasan abinda zai faru gobe (Wa’iyazubillahi), Kai tsaye zamuce wannan mutum ya karyata Allah da ManzonSa (Saww). Allah ya kyauta.

Cikin bayanan Wannan mutumen yayi Rantsuwa tafi a Kirya, Wanda wannan Ma fasikancine. Domin a cikin Rantsuwowin da malamai suka karkasa to kuwa yayi babba daga cikinsu.

Wannan rantsuwa itace, Al-Yaminul-Ghamus ((Rantsuwa mai halakarwa),  Wannan Rantsuwa malamai suka ce, ita ce: Rantsuwar da mutum zai yi ta akan karya domin cin hakkin wani. Saboda irin girman da wannan rantsuwar take da shi Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabba a gare shi ya ke cewa "Dukkan wanda ya yanki hakkin wani mutum musulmi da rantsuwar shi to hakika Allah ya wajabta mishi wuta kuma ya haramta mishi Aljanna" Muslim ya ruwaito shi, (A’uzubillahi min zalik).

Sannan dukkan wanda ya bi wannan mutumen ya yarda da zancensa shima ya sabawa Allah (SWT) domin  Allah yana cewa "Kada ka bi dukkan mai yawan rantsuwa, wulakantacce." Suratul-Kalam, aya ta 10).

Abu na gaba ko na karshe da zamfadi da ke nuna wannan mutumen bokane shine, KANYA ba ta daga cikin itacen da aka fada a cikin Al’qur’ani mai girma da Hadisan Ma’aiki (Saww), Ku lura bawai ina cewa tunda bata cikin Alqur’ani da Hadisai ba ba ina nufin bata magani bane A’a bahaka nake nufi ba

Shi wannan mutumen ya fadi cewa, KANYA ita kadaice Itacen da ta dade a duniya domin tun rowan Duhana Ma’ana zamanin Annabin Farkon Annabi Nuhu (Alaihis Salam)  take, Itace kai bata mutu ba.

Kai tsaye Wannan Karyane domin Kuwa, tunda babu shi a Alqur’ani da Hadisi to A ina ya samo haka? Ni dai nasan Jerin Itacen da suka zo a alqur’ani da Hadisai In ganttatu In shaaa Allahu zan samu Lokaci In kawo su kamar yadda Imamu IBN Khathir ya tattarosu a cikin littafinsa.

Abu na biyu da ke nuna wannan Mutum Boka ne shine, Yace, Ba’a dibar wannan Itace sai Ranar LITANIN (monday), to meye matsalar sauran ranakkun? Babu shakka wannan ire-iren sharuddan da Aljannu ke gin da yawa mutane masu huldayya dasu ne don haka muyi hattara.

Idan mutum ya ci gaba da amfani da Ire-iren wayannan Sharudda babu shakka ya Janyo ALJANNU su rika hulta da shine babu kakkautawa. Allah ya tsare mu. Don haka mu kula.

Please A turawa ‘yan Uwa domin Suyi HATTARA Domin Amfani da Ita Aikin Bokayene.

Jamilu Sani Rarah Sokoto
Sat 23/12/2017

Monday, 2 October 2017

SHIN A MALIYA (THE RED SEA) NE FIR’AUNA YA NUSTE? Fitowa ta farko



SHIN A MALIYA (THE RED SEA) NE FIR’AUNA YA NUSTE? Fitowa ta farko
******
Larabawa kan kira wannan teku da Bahar al-Ahmar Idan aka fassara zuwa Hausa kuwa sai a kira shi da (Bahar Maliya), Turawa kuma sukan kira wannan teku da “Red sea” wato jar teku. Kafin Jin shin ko anan ne Fi’auna ya nutse akwai bukatar Sanin Tarihin wannan teku kadan (Da yake wannan Teku na daga cikin tekunan duniya masu ban mamaki da marubuta da Masana Ilimin Kimiyya da yawa sukayi rubutu kan ta).
Turawa sun kira wannan wuri da Jar teku saboda yanayin jaja-jaja na tsaunukan da suke wannan wuri da ake kira Bahar-maliya.

Wani shahararren marubuci da ake kira da suna Mr E.M.Foster,ya bayyana cewa,tun tale-tale matafiya da yan safara wadanda suke ratsawa ta wannan teku, suka sa mata wannan suna “Red sea” ko kuma “Bahar-ahmar’’.

Wannan ruwa sune marraraba tsakanin yankin Afrika da kuma yankin Asiya. Ruwan wannan teku suna da tsawon kilomita 2000 sannan fadinsu ya kai kimanin kilomita 300. Zurfin su kuwa ya kai mita 2.500.

wayannan Ruwan suna iyaka da kasashe Takwas, wanda suka hada da kasashe hudu na Afrika, Masar, Eritrea,Jibuti, da Sudan,sai kuma ksashe hudu na yankin, Asiya Saudiya, Yamen, Israila da kuma Jordan.
Anyi ta muhawara akan wai me yasa ake kiran wannan teku da “Jar teku” Inda Wasu daga cikin marubutan kasar Birtaniya, da sukayi rubuce rubuce kan wannan Tekun sun tafi akan cewa, wannan suna na “Red sea’’ da Turawa suke kiran tekun Bahar maliya da shi, ba saboda yanayin jaja-jaja na tsaunuka bane, a’a, sakamakon yawan gamsakuka da take kewaye da gabar tekun wanda idan rana ta haska sai ta mai da tekun ta rinka daukar launin jaja-jaja ruwan dorawa-dorawa, da wasu kaloli daban wannan shine dalilin dayasa ake kiran ta da suna “Red sea’’ wato Jar-teku a hausance.

Masana ilimin kimiyya kuwa, sakamakon nazarin da wasu likitoci da kuma masana ilimin tarihi da halittun cikin ruwa suka gudanar,a shekarar 1646. Wani shahararren likita kuma marubucin litattafan turanci da ake kira da suna Sir Thomas Brown ne ya bayyana a cikin littafinsa cewa, wani masani akan halittun Ruwan-teku da ake kira da suna Sir Walter Raleigh, ya na kan ra’ayin cewa, Bahar maliya dai teku ce da take da launuka daban-daban, ya danganta da bangaren da mutum ya ke kallonta.

Sir Raleigh ya ci gabada bayyana cewa nazarin da yayi game da tekun baharmaliya ya tabbatar masa da cewar wannan teku tana da launuka daban-daban. Wani bangaren kore ne fatau,wani bangaren kuma zaka ganshi fari ne da ruwan dorawa-dorawa, wani gurimma ka gan shi shudi-shudi. Saboda haka kalar kowanne bangare na tekun ta dangantane da yanayin yashi ko kuma lakar da take acan kar kashin kasa.

Sai dai kuma har wa yau daya daga cikin malaman kimiyya kuma shahararren marubuci Carl Drews dan kasar Amerika shi ya musanta wancen zancen na Sir Thomas Brown Inda ya bayyana a cikin littafensa mai suna “Between Migdol and the Sea: Crossing the Red Sea with Faith and Science”, cewa, “ A’a, ruwan tekun maliya ba ja ba ne”. haka kuma ya musanya zance da wasu masana Ilmin Teku da Malaman Tarihi suka bayyana na cewa, A nan ne Allah (SWT) Ya halakar da Fir’auna da Jama’arsa lokacin da suka biyo Annabi Musa (AS).

In shaa Allahu Zan Dakata anan Sai mun hadu a Rubutu na Gaba da Iznin Allah.

Jamilu Sani Rarah Sokoto
02/10/2017


Monday, 3 July 2017

TARIHIN IMAMU ABU HANIFAH

TARIHIN IMAMU ABU HANIFAH
******

"Idan Karya Nakeyi To bayani na ya tabbata taya zaka dauki Matsayi na Alkalin Alkalai Ka bawa makaryaci?" Inji IMAMU ABU HANIFAH.

An Haifi Imamu Abu Hanifa a Cikin Birnin Kufa dake kasar Iraq a lokacin mulkin Kaliphancin Umayyad wato Abd al-Malik ibn Marwan. Mahaifinsa Dan kasuwane daga Kabul dake Afghanistan, mahaifin Imamu Abu Hanifa nada Shekara 40 a duniya aka haifeshi.

Asalin sunan sa An-Nu’uman bin Thabit, At-Taimi,  Abu Hanifa Na daga Cikin Manyam Malamai na farko farko da suka yiwa Musulunchi Hikima Bayan Sahabban Manzon Allah (Sallalahu ALaihi Wa'alihi Wasallam), Imamu Abu Hanifa ya rayayi rayuwa  kamar da Sahabbain Annabi (Sallalahu ALaihi Wa'alihi Wasallam), guda 4 daga cikinsu Akwai Anas Bin Malik, Jabir ibn Abd-Allah da kuma Sahl ibn Sa'd (RA).

An haifi Abu Hanifa Shekara 67 bayan Wafatin Annabi (Sallalahu ALaihi Wa'alihi Wasallam). Kuma Allah ya bashi basira tun yana yaro karami. Har an ruwaito Cewa, Watarana acikin garin Baghdad akwai wani babban kafiri wanda bai yarda da tauheedi ba, kuma bai yarda da cewa akwai Allah ba.
Har ma ya kirkiri wasu tambayoyi yana ta neman wanda zai amsa masa su. Duk Malaman garin sun kyaleshi basu daukeshi da muhimmanci ba.

Alokacin nan Imam Abu Hanifah (rah) yana yaro karami kwata-kwata bai fi shekara goma ba. Watarana yazo wucewa sai yaji mutumin nan yana da Ikirarin cewa wai Musulmai sun kasa amsa tambayoyinsa. Sai Imam Abu Hanifah ya matsa kusa dashi yace masa “In sha Allahu ni zan amsa tambayoyin naka komai wahalarsu”. Mutumin ya amsa gayyatar, Kuma Jama’a suka cika da mamaki. Ta yaya wannan ‘dan Qaramin yaro zai iya jayayya da Kafirin nan wanda manyan Maluma suka kasa ja dashi!

Da ranar Mukabalar tazo sai Jama’ar garin gaba daya suka taru a wani fili a tsakiyar garin Baghdad wanda dama anan ake gabatar da duk wani Muhimmin taro. Sai shi wannan kafirin ya hau kan tudun dake tsakiyar taro. Sannan ya bude muryarsa ya jefo tambayarsa ta farko zuwa ga Abu Hanifah; “Shin menene Allahn naku yake yi dai-dai yanzu? Abu Hanifah ya tsaya yayi tunani na ‘yan mintuna kadan, sai yace ma mutumin “To ina so kai ka sauko kasa, ni kuma in hau sama sannan in baka amsarka”. 

Wannan yaro karamin yaro ‘dan shekara goma (wato Imam Abu Hanifah) ya hau saman kan tudun sannan yace “Ya Allah kaine shaida gareni agaban duk wadannan Mutanen cewar na shaida lallai yanzun nan kai ka Qaddara saukowar wannan kafiri zuwa Qasa, kuma ka Qaddara cewar Mumini zai hau sama (wato zai daukaka akansa)”.

Da Mutane (‘yan kallo) suka ji wannan amsar ta fito cikin fasaha daga bakin Abu Hanifah, sai suka fara kabbara “Allahu Akbar!” Allahu Akbar!” Tun daga nan kafirin nan ya fara ganin kaskanci.
Amma sai ya sake jefowa tambayarsa ta biyu “Shin meke raye kafin Allahn naku?” (Subhanallah). Imam Abu Hanifah (rah) yayi tunani zuwa wani lokaci sai yace ma kafirin ya Qidaya masa lambobi daga goma zuwa Qasa Sai kafirin ya fara “Goma, tara, takwas, bakwai, shida, biyar, hudu, uku, biyu, daya, sufiri” Sai Imamu Abu Hanifa yace masa “Shin me ka gani bayan sufiri (wato zero)?”

Mutumin yace “Babu komai kafinsa, ni ban sani ba”. Da jin haka sai Imam yayi murmushi yace masa “To gashi nan ka riga ka bawa kanka amsa...Hakika Allah shine rayayye kuma dawwamamme. Babu kowa kuma babu komai kafinsa”. Daga wannan sai waje ya rude da kabbara, suna Qara jinjina ma Imam Abu Hanifah (rah). Kafirin nan zuciyarsa ta harzuka, ransa ya baci. Sai ya jefo tambayarsa ta Qarshe “SHIN YANZU WAJEN INA (WACCE KUSURWA) ALLAHN NAKU YAKE KALLO?” (Shin gabas yake kallo ko yamma ko kudu ko Arewa?). Imam Abu Hanifah bayan yayi tunani zuwa wani lokaci sai yace a kawo masa Fitila (Aci-balbal ko kuma kyandir). Da aka kawo masa sai ya damka wa kafirin nan. Yace masa ya kunna masa, Bayan kafirin ya kunna kyandir din sai ya tambayi Imam Abu Hanifa , to menene dalikin haka? Sai Imam Abu Hanifah yace masa “Shin wanne waje ne wutar hasken kyandir din nan take kallo?” Sai kafirin yace, “Tana kallon dukkan kuskuwoyi ne. (wato gabas, yamma, kudu, arewa, sama da Qasa) Babu inda bata kallo” Sai Imamu Abu Hanifa yace masa “Ai ka riga ka amsa tambayarka. Hakika Hasken Allah ya mamaye ko ina. Yana nan ako ina, babu wajen da babu shi”.

Daga nan sai mutane suka rude da kabbarori “Allahu Akbar! Allahu Akbar!! Allahu Akbar!!!”. Shi kansa wannan kafirin yayi mamakin ilimi da basirar Imamu Abu Hanifa (RA). Don haka anan wajen ya furta kalmar Shahada, ya zama Musulmi kuma ya zama Almajirin Imam Abu Hanifah (ra).

Imam Abu Hanifah yana daga cikin mutane mafiya kaifin hankali da basira daga cikin Maluman wannan al'ummar ta Musulunci. Watarana barayi sun shiga gidan wani mutum suka yashe masa dukiyarsa baki 'daya, sannan suka sanyashi ya rantse akan cewa ba zai tona musu asiri ba. Idan kuma ya tona asirinsu to Matarsa ta saku, Saki uku!! Wannan mutum ya wayi gari cikin tsananin bakin ciki. yana kallon mutanen nan suna ta sayar da kayansa da suka sato, amma bashi da damar yace komai, tunda ya riga ya rantse idan ya fallashesu to matarsa ta saku saki uku!! Saboda haka sai yaje ya gaya ma Imam Abu Hanifah halin da yake ciki. Sai yayi Murmushi yace masa "Na san hanyar da zamu bi, kayanka zai dawo ba tare da kace komai ba". Sai Imam Abu Hanifah yasa aka tara masa dukkan Limamai da ladanai na garin, sannan yace musu "Wannan mutumin anyi masa sata ne. amma shin kuna so dukkan kayansa ya dawo gareshi?". Suka ce "Eh". Sai yace to ina so ku tattaro min duk mutanen da aka ta'ba tuhumarsu da sata a unguwanninku.

Da aka tattarosu sai yasa aka kira masa Jami'an tsaro, yace musu ga wasu mutane nan zan rika tambayar wannan mutumin game dasu. Duk wanda kuka ji wannan mutumin yayi shuru bai ce komai akansa ba, to 'barawo ne. ku kamashi. Sai Imam Abu Hanifah yasa aka rika fitowa da mutanen nan 'daya bayan 'daya. Yana tambayar mutumin nan "SHIN WANNAN NE BARAWONKA?". Sai mutumin yace "A'a ba shi bane". Sai ace wannan ya wuce. Amma idan aka tambayeshi "SHIN WANNAN NE BARAWONKA? " in aka ji yayi shuru bai ce komai ba, sai Imam Abu yace "KU KAMA WANNAN SHIMA BARAWO NE".

Da haka sai da aka kama dukkan barayin nan ba tare da mai dukiyar ya ambaci sunayensu ba.
Allah Mai kyauta da karawa kamar Yadda Imamu Abu Hanifa Yake da kaifin basira haka Allah ya Azzurtashi da 'ya mai kaifin Basira. Abu Hanifa ya kasance yana karba tambayoyi tare da bada fatawowi hadi da karantarda dalibban Ilmi.

Wata Rana Sai aka yi masa wata tambaya wacce ta daure masa kai, tambayar kuwa itace; "ME YASA A MUSULUNCE SU MATA BA'A BASU DA DAMAR AUREN MAZA FIYE DA DAYA BA, ALHALI SU MAZA NA AUREN MACCE HAR UKKU?" Wannan tambayar ta daurewa Imam Abu Hanifa kai sosai da Sosai, Cen 'yarsa da ke Zaune Kusansa (wato Hanifa), Sai tace, "Ya Babana ai zan iya karba wannan tambaya Idan har ka amincemin."

Abu Hanifa Ya amince mata akan ta bada amsar wannan tambaya in har ta san amsa. Hanifa ta sa aka tara mata 4 ta bukaci a kawo katon masaki cike da nono, bayan an kawo wannan masaki, Sai tabawa kowace macce kofi daya tace kowacce ta debo wannan Nono dake cikin wannan Masaki. Bayan kowacen su ta debo (Wannan Nonon), Sai tace, dukansu su mayarda nonon a ciki. Dukansu suka sake mayarda nonon da suka diba. Sai Hanifa tace, "To kowaccen ku ta debo Nonon da ta zuba a cikin Wannan masaki, ba tare da ta debo wanda bata zuba ba."

Dukansu sai suka ce, "Taya zamu iya debo nonon da muka zuba kuwa? Alhali nonon ya hade?"
Sai Hanifa Tace, "To kamar hakane, Idan macce ta auri maza biyu ko ukku ko hudu, aka haihu ba za'a iya gano waye mahaifin jarinrin ba." Wannan Amsa ta Sanya Numan bin Thabit (Abu Hanifa) farin Ciki, daga nan sai aka rika kiransa da sunan (Baban Hanifa).

A shekarar 763, Imamu Abu Hanifa ya samu takardar Bukatar yayi Jagorancin alkalin Alkallai daga Al-Mansur a zamanin Kaliph Harun al-Rashid. Lokacin da Wannan takarda ta sami Abu Hanifa sai ya Rubutawa Al-Mansur Cewa, "Hakika ni Ban cencancan ci Zama kan wannan Mukamin ba abawa wani." Lokacin da Sako ya Zowa Sarki Al-Mansur sai ta yasa aka kira masa Imamu Abu Hanifa Yace Masa Me yasa ba zaka Amsa ba? Abu Hanifa Yace, Ban Cen-centa bane kawai.

Al-mansur Ransa ya bace Yace, "Hakika Karya Kake yi domin ka cen-centa." Sai Imamu Abu Hanifa Ya buda baki yace, "Babu Shakka bayani na ya tabbata (ban Cen-centa ba), taya zaka dauki Matsayi na Alkalin Alkalai Ka bawa makaryaci?" Wannan amsar ta Abu Hanifa Ita ta harzuka wannan Sarkin nan take ya sa aka kama Imamu Abu Hanifa aka Rufeshi a Gidan kaso (Prison) aka Rika azabantar dashi azaba kala-kala a gidan yarin. 

Duk da Irin Azabar da Imamu Abu Hanifah yake sha masana tarihi sun tabbatarda ci gaba kawai yayi da karantarwa da yin Kira zuwa a kadaita Allah a Cikin Wannan Gidan kaso. A karshe dai wasu malaman tarihi sun bayyana a gidan yarin Allah ya karbi ransa.
Masana tarihi suka ce kusan mutum dubu hamshin (50,000), ne suka halarci zana'Izarsa a lokacin da Allah Yayi Masa Cikawa.

Daga cikin littafan da ya wallafa akwai, Fiqh al-Akbar; Fiqh al-Abasat Kitaab-ul-Aathaar, Kitabul Aathaar, Musnad Imaam ul A'zam, da kuma Kitaabul Rad alal Qaadiriyah. Imam Abu Hanifa ya hardace hadisai masu yawan gaske har an ruwaito wani daga cikin magabata na cewa, Imamu Abu Hanifah ba ya rawaito hadisi sai wanda ya haddace, ba ya rawaito hadisin da be haddace ba. Imam Abu Hanifa ya rasu a shekarata (150A.H).

Jamilu Sani Rarah Sokoto
Mon 17-04-2017

Saturday, 22 April 2017

GUDUMMUWAR MAWAKAN HAUSA A CIKIN AL-UMMA

GUDUMMUWAR MAWAKAN HAUSA A CIKIN AL-UMMA
******
Sau tari Wasun mu sukan Rik'ajin haushi tare da Sukar mawaka musamman namu na Hausa tare da yi musu kallo a matsayin 'yan Iska ko kuma masu b'ata tarbiyar Al-ummah. Hak'ik'a kafin In kawo gudummuwar da suke bayarwa yana da kyau in yi bayanin wata aya a cikin al-qur'ani wacce wasu da yawa basu san dalilin Saukar taba, amma daga zarar Sunji anyi maganar mawaki sai su kawo ayar a matsayin Hujjar Qin wak'a. Ayar da take Cikin Suratush-Shu'ara'I aya ta 224 In da Allah (Swt) Yake Cewa; "WASH-SHU'ARA'U YATBA'UHUMUL-GH AAWUUN" Ma'ana "Kuma mawaƙa halakakku ne ke bin su." (Sura shu'ara'i aya ta 224).

Ibn Jareer da Ibnu Abi-Haatim sun fitar da hadisin daga Babban Malami Masani tafsirin al-qur'ani wato Ibnu Abbas cewar; Wasu mutane (mawaqa) su biyu sunyi ma juna habaici (alokacin Manzon Allah (Saww), Daya daga cikinsu mutumin madina ne. Dayan kuma ba d'an madina bane. Sun kasance a koda yaushe sukan soki junansu da munanan kalamai a waken da suke, kuma kowannensu yana da masu binsa suna zuga shi daga cikin danginsa.

Sai Allah (Swt) Ya Saukar da fadinSa Cewa, "Kuma mawaƙa halakakku ne ke bin su." To wayancen dangin nasu sune Allah yake nufi da "Halakakku" (su da ke zugi domin ayi zage-zage).
Har wayau Imamul-hakim da Ibnu Jareer sun karbo hadisi daga Abu Hasan Albarrad cewar: "bayan da wannan ayar ta sauka wash-shu'ara'u. Sai Wasu daga cikin mawakan Annabi (Saww), Irinsu Abdullahi Ibn Rawaha da Ka'abu Ibn Malik da kuma Hassanu Ibn Thabit (rta) suka je wajen Manzon Allah (saww) suka ce: "Ya Rasulil Lahi Gashi Wannan aya ta Sauka, Kuma Allah yasan Cewar, Mu mawaka ne. Shikenan mun halaka." Nan da nan sai Allah (Swt) ya sake Saukarda wata ayar Inda Allah (swt) yayi istisna'i garesu cewar. "ILLAL-LADHEENA AMANU" ma'ana "Sai dai wadanda sukayi imani kuma suka aikata ayyuka na kwarai kuma suka yi zikirin Allah da yawa" (Shura'I aya ta 227). Sai Manzon Allah (Saww) ya kirawo su ya gaya musu tare da karanta musu Ayar domin hankalinsu ya kwanta.

Mai Neman karin bayani ya duba, Usudul-ghaabah- Juzu'i na 3 shafi na 235. Tirmidhy ma ya fitar da hadisin ta isnadi mai Qarfi, a duba a Sunanut-Tirmiziy hadisi mai lamba 2851 da kuma SIYARU A'ALAMIN-NUBALA 'I juzu'i na 1 shafi 236 domin karin bayani. Nasan wani zaice to ai Wakokin Hausawa babu komai a cikin su in ban da sakarci da sharholiya da kuma son a kwaikwayi Indiyawa, Babu shakka duk mai irin wannan tunani zan iya kiran shi wanda bai waye ba ko kuma ma bai da zurfin tunani domin wakokin Hausa suna taka muhimmiyar gudummawa ga addinin musulunchi da ma al'umma a kebe.

Muna sane da cewa kafin finafinan Hausa su samu babu finafinan da suka fi na Indiyawa karbuwa a kasar Hausa, kuma idan an duba za a ga akwai wakokinsu wadanda babu komai a ciki face yabon gumakansu da sauran abubuwan bautarsu, to ire-iren wadannan wakoki ne mutanenmu suke yi da bakinsu, ba su san mene ne ma’anar abubuwan da suke fada ba, amma wakokin da ake yi a finafinan Hausa kowa ya san abin da ake fada, sannan ana ambaton Ubangiji da Annabinsa da kuma yabo gare su, kafin a shiga gundarin wakar ko a tsakiyarta ko kuma a karshenta (Wanda ake kira Introduction and Conclusion a turance). Wannan ba karamar gudumuwa bace domin da yanzu Allah kadai ya san wanda ya hardace wakokin bautar gunka. Mu Janye maganar Gudumuwa wak'a na da tasiri a wajen jan hankalin al'umma daga cikin mawakan a zamanin Annabi (Saww) akwai Hassanu bin Thabit (rta) kamar yanda na ambata a baya, Babu shakka Annabi (Saww) da kansa ya tab'a umurtarsa da ya tashi ya mayarwa da wasu mawaka da suka ci mutunchin Annabi (Saww) da martani.

Bayan wancen K'arnin Bincike ya nuna cewa, mutum na farko wanda ya fara rubuta littafi a kan ilimin ma'aunin waka wanda da Larabci ake kira Arudhi shi ne Khalil Ibn Ahmad Alfarahidi Albasari, a karni na biyu. Marubucin ya rasu a shekara ta 174 bayan hijira Annabi Mahamadu (Saww) wacce ta zo daidai da shekarar ta 791 Shekarar alak'ak'ai Miladiya. To, amma kuma tarihi ya nuna cewa, kafin shi wannan bawan Allah ya rubuta wannan littafi akwai mawaka da suke rubuta wakoki, ko da ya zo ya rubuta wannan littafi sai ya dace da ma'aunin ire-iren wakokin da suke yi tun dauri. Dalilin da ya sa ya rubuta wannan littafi shi ne, Khalil ya yi kwadayin ilmi irin na Sibawaihi wani malamin Nahawu ko kuma marubucin Nahawu, sai ya fita yana kewaya Ka'aba yana rokon Allah ya ba shi baiwa ta ilmi, sai Allah ya yi masa baiwa ta wallafa littafin ilmin ma'aunin waka, Arudhi. A cikin littafin ne ya takaita waka a kan ma'auni goma sha shida. To, amma da yake rubutun nawa ba yana magana a kan ilimin wakar ba ne, bari na mayar da alkalami na a saman hanya, wato kar ya yi ratse.

Amma ya yakamata a yi wakar? Kasancewa a al'adar bahaushe tana tafiyane tare da addinin musulunce, to kamata yayi idan za'a yi wakar ta kasance namiji ne kadai ke rairata banda macce, haka idan macce za'a nuna tana wakar to kada a hada ta da namiji. Misali, akwai wani fim mai suna Wani Gari. A fim din ai ba'a hada mata da maza suna rawa ba, kawai an nuna jarumin ne shi kadai yana karanta wakar. Haka a fim din Salma shima jarumin ne kawai ke waka banda macce, haka fim din Jiddah shima macce ce kadai ke wakar ba tare da namiji ba. haka ya kamata wakokin finafinan Hausa su kasance domin kare mutuncin al'adar mu da kuma addinin mu.

Babu shakka ina goyon bayan Wakoki da finafinan Hausa sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba nuna saurayi da budurwa suna waka da rawa a tare wannan sam ba al'adar Hausawa ba ce sam domin duk wanda ya kalli irin wa dannan wakoki a finafinan Hausa zai ga abin sam ba tsari. sai da me kuma? masu kallo ne ke sanya ana sanya saurayi da budurwa a tare domin su a ganinsu idan ba haka akayi ba sam ba'a burgesu ba. saura Gudumuwar fina-finan Hausa.

Jamilu Sani Rarah Sokoto
Sat 22-04-2017

Friday, 21 April 2017

DALILAN DA KE NUNA SAMUWAR ALLAH (SWT), ZUWA GA ATHEIST.

DALILAN DA KE NUNA SAMUWAR ALLAH (SWT), ZUWA GA ATHEIST.
*****
Zuwa ga Masu da'awar Cewa, Babu UBANGIJI (Swt), Atheist a turance ku sani Duniyar nan gaba d'ayanta tana mai tabbatarwa da shaidawa da fad'in cewa, akwai Allah Mai girma da buwaya.

A cikin Al-qur'ani Mai Girma Allah Madaukakin Sarki yana cewa,“Manzanninsu suka ce, yanzu akwai shakka a cikin samuwar Allah, wanda ya halicci sammai da qassai, yana kiranku don ya gafarta muku zunubanku ya jinkirta musu zuwa wani lokaci sananne. Sai suka ce, kufa ba kowa ba face
mutane kamar mu, kuna so ne ku kange mu daga abin da iyayenmu suke bautawa, ku zo mana da wata hujja mabayyaniya” (Suratul Ibarahim aya ta 10).

Hakika Mumini shi ke da yaqinin cewa, Allah Madaukakin Sarki shi ne Ubangiji, mai iko, ya kuma tabbatar da cewa shi ne abin bautawa shi kadai. Ta yaya zaku tsaya akan neman dalili akan samuwar abin da shi ne dalilin samuwar komai da kowa? Idan muka haura zuwa ga dalilan da suke nuna samuwar Allah, za mu samu dalilai masu yawa kamar haka:

DALILIN SAMUWAR ALLAH NA FIQRA: Babu wani abu da za ka yabi Allah da shi face da falalarsa da ni’imominsa, a kowane hali kana buqatar Allah mai girma da buwaya. Asalin halitta an yi ta ne a kan imani da Allah mahalicci. Babu wanda yake barin wannan abin da aka halicce shi a kai na imani da Allah mahalicci sai wanda Allah ya rufewa zuciya da hankali.

Daga cikin manya-manyan dalilai da suke nuna an halicci mutum a kan imani da samuwar Allah Mad'aukakin Sarki Shine, fad'in Manzon Allah (Saww) cewa, “Dukkan wanda ake haihuwa ana
haihuwarsa akan asalin halitta, iyayensa ne suka mayar da shi bayahude ko banasare ko ba majuse, kamar irin yadda dabba take haihuwa, shin kuna ganin ana haihuwar dabba mai yankakken kunne?” (Imamu Bukhari ne ya rawaito sh).

Dukkan wani abin halitta ya yarda da kadaita Allah a yanayin halittarsa Allah (Swt) ya ce, “Ka tsayar da fuskarka a kan addini, kana mai karkata ga barin qarya.Halittar Allah ce da ya halicci mutane a kanta, babu canji ga halittar Allah. Wannan shi ne addini miqaqqe sai dai da yawan mutane ba su sani ba” (Suratur rum aya ta 30). Wad'annan dalilai na hankali suna nuna samuwar Allah mad'aukakin Sarki.

Sai tabbatuwar da samuwar Allah a hankalce ya fi kowane dalili qarfi ga duk wani wanda shaidanu ba su janye shi ba, a cikin Al-qur'ani mai girma Allah Mad'aukakin Sarki yana cewa, “Halittar Allah ta asali da ya halicci mutane a kanta” (Suratur rum aya ta 30). Bayan ya ce “Ka tsayar da fuskarka ga addini kana kaucewa barna”. (rum : 30).

Sunan Allah suna ne da aka zana shi a cikin halittar kowa, ba ya buqatar wani dalili fiye da wannan.
Lafiyayyen hankali yana shaida wa da samuwar Allah, amma wanda shaidanu suka janye shi zai iya qin wannan dalili ya ji ba ya buqatarsa. Amma idan ya fada cikin wata matsala babba, sai ka ga hannayensa da idanuwansa da zuciyarsa sun nufi sama kai tsaya suna neman taimako da agaji daga Ubangijinsa. Domin ya koma halittarsa ta asali madaidaiciya.

DALILIN SAMUWAR ALLAH NA HANKALI: Daga cikin manya-manyan dalilai masu qarfi, wadanda ba wanda zai yi musu akansu sai mai jayayyar runto kadai, akan tabbatar da samuwar Allah mahalicci, daga cikinsu akwai

1-Dukkan halitta akwai wanda ya halicceta: dukkan wad'annan ababen halitta gaba d'ayansu akwai wanda ya samar da su, domin ba zai yi wu su samar da kansu da kansu ba, saboda babu
abin da ya halicci kansa, don kuwa babu shi kafin samuwarsa, to kuma ta yaya zai samar da kansa, don dukkan wani abu samamme akwai wanda ya samar da shi.

Sannan kuma samuwar wadannan abubuwa akan wannan tsari mai kyau, hadadde, mai tafiya tare da sababi, a hade da juna, ba zai yiwu ba a ce haka kurum abun ya faru kwatsam, a’a dukkan wani mahaluki ba makawa yana da wanda ya halicce shi. To idan kuwa abin haka yake, to lallai Allah ne Ubangijin talikai ya samar da su, Allah Mad'aukakin Sarki ya fad'i wannan dalili inda yake cewa “Shin an halicce su ne daga babu, ko kuwa su ne masu yin halittar?” (Suratud Dur aya ta 35).

Allah yana nufin su ba haka kurum akan halicce su ba, ba tare da wani wanda ya halicce su ba, kuma ba su suka halicci kawunansu ba, to dole suna da wanda ya halicce su, wanda shi ne Allah Madaukakin Sarki.
Don haka ma a lokacin da Sayyidina Jubairu d'an Mud’im (RA) ya ji Manzon Allah (Saww) yana karanta suratud Duri, ya zo kan wadannan ayoyi, inda Allah yake cewa, “Shin an halicce su ne daga babu, ko kuwa su ne masu yin halittar. Ko su ne suka halicci Sammai da Qasa, a’a ba su yi yaqini ba. Ko a wajensu akwai taskokin Ubangijinka, kai ko su ne wadanda suka mamaye komai” (Suratud Dur aya 35 zuwa 37).
A lokacin Jubairu yana mushiriki bai musulunta ba, amma duk da haka sai ya ce, “Zuciyata ta kusa ta tsinke na musulunta” (Bukhari ne ya rawaito shi).

Dan adam tare da dimbin ilimin sanin duniya da Allah ya ba shi, har yanzu ya kasa gano wasu abubuwa na boye wadanda babu abin zai kawo qarshen cece-kuce a kansu sai kawai imani da akwai Allah shi kadai.
2-Bayyanannu ayoyin Allah a cikin duniya da halittarsa. Allah Madaukakin Sarki ya ce, “Ku duba (ku yi tunani) mene ne a cikin Sammai da Qasa” (Yunus : 101).

Saboda a cikin duba sammai da qasa zai bayyana Allah ne mai halitta, kuma ya qara tabbatar da
kadaituwar Allah da ayyukansa. An cewa wani mutumin qauye, dame ka gane Ubangijinka? Sai
ya ce, “Alamar sawu tana nuna tafiya, kashin raqumi yana nuna akwai raqumin. To yanzu sama
mai matakalai, da qasa mai hanyoyi, da teku mai igiyar ruwa da yawa, yanzu wadannan ba za su
nuna akwai Allah mai ji mai gani ba?”.

3-Tsaruwa lamarin duniya da kyautatuwarsa, dalili ne akan wanda yake tsara shi, shi ne abin
bauta shi kadai, kuma mamallakinsa shi kadai, Ubangiji shi kadai, babu wani abin bauta sai shi, kamar yadda ba zai yi wu ba a samu Ubangiji biyu, masu halitta kuma wadanda suka yi daidai da juna, to haka ma ba zai yiwu a samu ababen bauta guda biyu ba, waxanda suka yi daidai da juna.

Kuma ba zai yi wu a samu wadanda suka yi duniya su biyu ba, abu ne tabbatacce a hankali, to haka ma ba za a samu abbaben bautawa guda biyu ba.

DALILIN SAMUWAR ALLA NA SHARI'A: Dukkan Shari’u suna nuna samuwar wanda ya yi halitta, kuma suna nuna cikar iliminsa da hikimarsa da jinqansa, saboda dukkan shari’u ba makawa da wanda ya shar’anta su, wanda shi ne Allah Mai girma da buwaya, Allah (Swt) yana cewa, “Ya ku mutane ku bautawa Ubangijinku wanda ya halicce ku, da wadanda suke gabaninku ko kwa samu taqawa. Wanda ya sanya muku qasa ta zama shimfida gareku, ya sanya kuma sama ta zama gini gareku, ya saukar daruwa daga
girgije, ya fitar da ‘ya’yan itace arziqi gareku, to kada ku sanya wa Allah abokan tarayya alhali kuna sane” (baqra aya ta 21 zuwa 22).

DALILIN SAMUWAR ALLAH NA JI DA GANI: Daga bayanannun dalilai da suke nuna samuwar Allah Mahalicci akwai dalilin da duk mai hankali yake gani kuma yake jinsa, kamar:

1-Amsa addu’o’i: Mutum yana roqon Allah, ya ce, “Ya Ubangiji” ya roqi wani abu, sai kuma ya ga an amsa masa, to wannan dalili ne da ake gani dake nuna samuwar Allah Ubangiji, saboda Allah ya amsa masa, kuma mutum ya ga hakan quru-quru.

Haka ma muma sau da yawa mun ji misalai a da, da yanzu na cewa Allah ya amsa musu abin da suka roqa. To wannan wani lamari ne da yake nuna samuwar Allah Mahalicci, a cikin Alqur’ani akwai dalilai irin wadannan da yawa, daga cikinsu akwai fad'in Allah, “Ka tuna (Annabi) Ayyuba lokacin da ya kira Ubangijinsa cewa cuta ta shafe ni, Allah kuma kai ne mafi jinqai masu jinqai. Sai muka amsa masa” (Al’anbiya aya ta 83 zuwa 84). Da ayoyi da yawa irin wad'annan. Kore samuwar Allah cuta ce a cikin hankali, kuma matsala ce a cikin tunani.

2-Shiryar da halittu zuwa ga abin da yake shi ne sirrin rayuwarta. Wanene ya shiryar da mutum zuwa ga kama mama yayi da aka haife shi? Wanene ya shiryar da Al-Hudu-Hudu har yake gane wurin ruwa a qarqashin qasa, wanda ba wanda yake ganin hakan sai shi? Haqiqa Wannan aikin Allah ne, yana cewa: “Ubangijinmu wanda ya halicci dukkan komai kuma ya shiryar da shi” (Daha aya ta 50).

3-Ayoyin da Allah ya aiko Annabawa da Manzanni da su, su ne Mu’ujizozin da Allah ya qarfafa su da su, ya zabe su, daga cikin mutane ya fifita su. Dukkan wani Annabi Allah ya aiko shi da wata mu’ujiza zuwa ga mutanensa, tana tabbatar da cewa abin da aka aiko shi da shi daga wajen Allah ne, mahalicci abin bauta shi kadai, babu wani abin bauta wanda ba shi ba.

Sannan har wayau daga Cikin dalilai na hankali da ke nuna Samuwar Allah (Swt), akwai yin Arziki ko talauci, babu shakka duk wanda zai ce babu Allah to yana Fadar son ransa ne. Domin idan ka duba a kusa da kai a kwai mai kuddi ko Ilmi wanda kake burin Inama ace kai ne, makawar kuwa kai ka halicci kanka to zaka Mayarda kanka kamar wancen da kake muradin zama kamarsa.

Abinda Zan Cewa, Masu da'awar Babu Allah d'aya ne Zuwa Biyu, Na farko Ina yi musu murna da Suka Shaidi Cewa, Babu Allah. Dalili kuwa Yana daga Cikin Sharuddan Karbar Addinin Musulunchi wato La'Ilaha (ma'ana "Babu Wani abin Bauta") don haka ina jan hankalinsu tun lokaci bai kire ba Su karbi ragowar ILLALLAH (ma'ana "Sai Allah").

Ina Fatan Duk wanda Ya Samu Karanta wannan Rubutun Zai taimaka da Share domin Wayannan mutanen suna nan Suna ta Jan yan Uwanmu a cikin wannan muguwar Ak'ida ta BABU ALLAH.

Jamilu Sani Rarah Sokoto
Thu 20-04-2017

KUYI HANKALI DA 'YAN DAMFARA

KUYI HANKALI DA 'YAN DAMFARA
******

A Ranar 07 ga watan Mayun Shekarar 2014 Jaridar Khaleej Times ta k'asar Dubai ta Ruwaito Labarin Wata Makekiyar damfara da aka yiwa Wata Mata 'yar k'asar Dubai Dirham miliyan hudu, wanda ya yi daidai da Naira miliyan 160 a kuddin Nageriya.

An damfari wannan matar ne don a cire wa ’yarta aljanin da ya hana ta aure. Jaridar ta Ruwaito Cewa, Al’amarin ya samo asali ne a lokacin da matar ta shiga damuwa, ganin cewa tsararrakin ’yarta sun yi aure, amma ita 'yarta ko labari babu. Da ta shiga tunanin yadda za ta aurar da ’yarta, sai kawar yarinyar ta nuna mata cewa akwai wata amtsala a cikin al’amarin ’yarta, inda ta nuna mata cewa aljani ne ya aure ta. Ita kuwa jin haka, sai ta yarda. Daga nan sai aka nuna mata cewa za a samo mata maganin aljanin da ya hana ’yarta aure.

Bayan kwanaki kadan, sai aka bayyana mata cewa aljanin da ya auri ’yarta yana da tsananin kishi, don haka ba zai kyale kowa ya aure ta ba. Kuma shi yake korar duk wanda ya nuna yana son ’yarta.
An dai cusa wa matar ra’ayin ta tuntubi wata bokanya, wadda ta bukaci ta ba Dirhami miliyan guda wato daidai da Naira miliyan 40. Wannan bokanya, sai ta kara da cewa abin wuyanta ma aljani ya kama shi. Don haka aka ce ta bayar da abin wuyan, wanda kimarsa ta kai Dirham dubu 700.

Bayan da ta aikata abubuwan da aka bukaci ta yi, sai kuma bokanya ta bukaci ta biya wasu dirhami miliyan biyu da dubu 700, don gudanar da wannan gagarumin aiki na cire aljani. “Wanda Jimlar kudin da bokanya ta bukaci a biyata sun kai Dirhami miliyan hudu (Naira miliyan 160),”.

Jaridar ta Khaleej Times, ta ruwaito cewa, wannan mata ta yi yunkurin sayar da gidanta, don haka ta bayar da cikon kudi na tsawon lokaci, inda za a dauki shekaru har zuwa 20 tana biyan kudin. Sai kawai aka aiko mata da sammaci, wai ana binta bashi.

Ganin haka, sai ita ’yarta suka kai kara gaban hukuma, aka kuma bincika, aka gano cewa, matar da ta yi musu wannan kulle-kullen an sha kama ta da laifin damfara. Hukumar Shari’a ta birnin Abu Dhabi ta bayar da cikakken rahoton damfarar, inda ta bayyana cewa,tuni matar ta bukaci hukuma ta dakatar da biyan wannan ciken kudin, a kuma soke amfani da shi kacokam.

Wannan Labarin Ya dade da faruwa, amma dalilin da ya sa na kawo shi shine, yanzu wasu mayaudara sun fara yawo a cikin wannan k'asa ta nigeriya da sunan bada magani. Yanda suke yi Shine, Idan suka zo a Unguwa Zasu tambaya Waye mai kuddi sosai a wannan Unguwar? Idan aka nuna musu sai su tambayi sunan 'yarsa Ko matarsa. Idan aka gaya musu sai su samu farar Leda su cika ta da Iska makil suyi Tsibbace-Tsibbacensu Da sunan matar ko 'yar Mutumen.

Nan take Ita kuma wacce aka yi wa wannan Asiri abin zai kama ta Sai cikinta ya Cika kamar Zai fashe, tare da Jin Matsanancin Jiri. Za'ayi ta neman magani amma ba za'a dace Ba, kuma su wayannan macuta sukan Sicce Wannan Cikin yau gobe kuma su Sake Hura shi.

Bayan Sati d'aya ko biyu zasu bayyana a Gidan da sunan Su masu bada magani ne zasu taimaka, A haka zasu kawo magani su bayar tare da Sanya miliyoyin kuddin da za'a bayar Idan ta samu sauki. Bayan kwana biyu sai suje su Sacce wannan ledar marar lafiyar ta dawo kamar bata tab'a ciwon ba. Wannan fa Shine damfarar da ake yi a yanzu.

Ina Mafita? Idan Irin Wannan Ya Faru a Unguwarku Ga Wata Mafita Da Ta tabbata daga Sunnar Manzon Allah (Saww). Za'a samu Fitsarin Rakumi da Nononsa a Rik'a bata tana sha In shaa Allahu Allah zai Cubutar da mai lalurar daga Makircin Wayannan Masihirta.

An Samo hadisi daga Manzon Allah (Saww) yace, Ku nemi nonon rakumi yana maganin duk wata cuta da ke cikin ciki. Haka Kuma An karbo daga Annabi (Saww) Yace: Nonon rakumi da fitsarin rakumi suna maganin cutar dake cikin ciki wadda ake kira (Dharibah).

Har Wayau Jaridar Emirati mai lamba 11172 wacce ta fito a shekarar fabairu 2006 ta rubuta wani bincike da tayi akan Rakumi inda ta kawo cewa abu mafi amfani da yake jikin Rakumi akwai nononsa yana tasiri wajen maganin ciwon zuciya da narkar da abinci da cututtuka da suka shafi daji da sauran cutuka.
A wani bincike da Dr Ahlam al-awadi yayi wanda magazine na al-da'awa suka buga mai lamba 1938 a shekarar 2004 ya ce, akwai amfani mai yawa a cikin nonon Rakumi daga cikin abinda ya kawo ya tabbatar da cewa fitsarin Rakumi na yana taimakwa wajen maganin cutar da ta shafi fata yana gyra ga shi ya sanya shi kyalli da laushi ya kuma fidda amosarin kai. Haka Kuma Fitsarin Rakumi Yana Maganin Kambun Baka da Sihiri Da Iznin Allah. Abin Lura Dai wannan ya faru da Wasu 'yan Uwa kuma Mashaa Allahu an samu waraka.

Note: Dharibah wata cuta ce dake cikin ciki, idan anci abinci baya narkewa har sai ya rube. To idan an sha nonon rakumi bayan an gama cin abinci, yana gusar da
wannan matsalar.
Wannan Damfarar Tuni na dade da Sanin ta Sai dai Yanzu abin ya fara Yawaita don Haka a Kula Jama'ah.

Jamilu Sani Rarah Sokoto
Thu 20-04-2017