Monday, 2 October 2017

SHIN A MALIYA (THE RED SEA) NE FIR’AUNA YA NUSTE? Fitowa ta farko



SHIN A MALIYA (THE RED SEA) NE FIR’AUNA YA NUSTE? Fitowa ta farko
******
Larabawa kan kira wannan teku da Bahar al-Ahmar Idan aka fassara zuwa Hausa kuwa sai a kira shi da (Bahar Maliya), Turawa kuma sukan kira wannan teku da “Red sea” wato jar teku. Kafin Jin shin ko anan ne Fi’auna ya nutse akwai bukatar Sanin Tarihin wannan teku kadan (Da yake wannan Teku na daga cikin tekunan duniya masu ban mamaki da marubuta da Masana Ilimin Kimiyya da yawa sukayi rubutu kan ta).
Turawa sun kira wannan wuri da Jar teku saboda yanayin jaja-jaja na tsaunukan da suke wannan wuri da ake kira Bahar-maliya.

Wani shahararren marubuci da ake kira da suna Mr E.M.Foster,ya bayyana cewa,tun tale-tale matafiya da yan safara wadanda suke ratsawa ta wannan teku, suka sa mata wannan suna “Red sea” ko kuma “Bahar-ahmar’’.

Wannan ruwa sune marraraba tsakanin yankin Afrika da kuma yankin Asiya. Ruwan wannan teku suna da tsawon kilomita 2000 sannan fadinsu ya kai kimanin kilomita 300. Zurfin su kuwa ya kai mita 2.500.

wayannan Ruwan suna iyaka da kasashe Takwas, wanda suka hada da kasashe hudu na Afrika, Masar, Eritrea,Jibuti, da Sudan,sai kuma ksashe hudu na yankin, Asiya Saudiya, Yamen, Israila da kuma Jordan.
Anyi ta muhawara akan wai me yasa ake kiran wannan teku da “Jar teku” Inda Wasu daga cikin marubutan kasar Birtaniya, da sukayi rubuce rubuce kan wannan Tekun sun tafi akan cewa, wannan suna na “Red sea’’ da Turawa suke kiran tekun Bahar maliya da shi, ba saboda yanayin jaja-jaja na tsaunuka bane, a’a, sakamakon yawan gamsakuka da take kewaye da gabar tekun wanda idan rana ta haska sai ta mai da tekun ta rinka daukar launin jaja-jaja ruwan dorawa-dorawa, da wasu kaloli daban wannan shine dalilin dayasa ake kiran ta da suna “Red sea’’ wato Jar-teku a hausance.

Masana ilimin kimiyya kuwa, sakamakon nazarin da wasu likitoci da kuma masana ilimin tarihi da halittun cikin ruwa suka gudanar,a shekarar 1646. Wani shahararren likita kuma marubucin litattafan turanci da ake kira da suna Sir Thomas Brown ne ya bayyana a cikin littafinsa cewa, wani masani akan halittun Ruwan-teku da ake kira da suna Sir Walter Raleigh, ya na kan ra’ayin cewa, Bahar maliya dai teku ce da take da launuka daban-daban, ya danganta da bangaren da mutum ya ke kallonta.

Sir Raleigh ya ci gabada bayyana cewa nazarin da yayi game da tekun baharmaliya ya tabbatar masa da cewar wannan teku tana da launuka daban-daban. Wani bangaren kore ne fatau,wani bangaren kuma zaka ganshi fari ne da ruwan dorawa-dorawa, wani gurimma ka gan shi shudi-shudi. Saboda haka kalar kowanne bangare na tekun ta dangantane da yanayin yashi ko kuma lakar da take acan kar kashin kasa.

Sai dai kuma har wa yau daya daga cikin malaman kimiyya kuma shahararren marubuci Carl Drews dan kasar Amerika shi ya musanta wancen zancen na Sir Thomas Brown Inda ya bayyana a cikin littafensa mai suna “Between Migdol and the Sea: Crossing the Red Sea with Faith and Science”, cewa, “ A’a, ruwan tekun maliya ba ja ba ne”. haka kuma ya musanya zance da wasu masana Ilmin Teku da Malaman Tarihi suka bayyana na cewa, A nan ne Allah (SWT) Ya halakar da Fir’auna da Jama’arsa lokacin da suka biyo Annabi Musa (AS).

In shaa Allahu Zan Dakata anan Sai mun hadu a Rubutu na Gaba da Iznin Allah.

Jamilu Sani Rarah Sokoto
02/10/2017


Monday, 3 July 2017

TARIHIN IMAMU ABU HANIFAH

TARIHIN IMAMU ABU HANIFAH
******

"Idan Karya Nakeyi To bayani na ya tabbata taya zaka dauki Matsayi na Alkalin Alkalai Ka bawa makaryaci?" Inji IMAMU ABU HANIFAH.

An Haifi Imamu Abu Hanifa a Cikin Birnin Kufa dake kasar Iraq a lokacin mulkin Kaliphancin Umayyad wato Abd al-Malik ibn Marwan. Mahaifinsa Dan kasuwane daga Kabul dake Afghanistan, mahaifin Imamu Abu Hanifa nada Shekara 40 a duniya aka haifeshi.

Asalin sunan sa An-Nu’uman bin Thabit, At-Taimi,  Abu Hanifa Na daga Cikin Manyam Malamai na farko farko da suka yiwa Musulunchi Hikima Bayan Sahabban Manzon Allah (Sallalahu ALaihi Wa'alihi Wasallam), Imamu Abu Hanifa ya rayayi rayuwa  kamar da Sahabbain Annabi (Sallalahu ALaihi Wa'alihi Wasallam), guda 4 daga cikinsu Akwai Anas Bin Malik, Jabir ibn Abd-Allah da kuma Sahl ibn Sa'd (RA).

An haifi Abu Hanifa Shekara 67 bayan Wafatin Annabi (Sallalahu ALaihi Wa'alihi Wasallam). Kuma Allah ya bashi basira tun yana yaro karami. Har an ruwaito Cewa, Watarana acikin garin Baghdad akwai wani babban kafiri wanda bai yarda da tauheedi ba, kuma bai yarda da cewa akwai Allah ba.
Har ma ya kirkiri wasu tambayoyi yana ta neman wanda zai amsa masa su. Duk Malaman garin sun kyaleshi basu daukeshi da muhimmanci ba.

Alokacin nan Imam Abu Hanifah (rah) yana yaro karami kwata-kwata bai fi shekara goma ba. Watarana yazo wucewa sai yaji mutumin nan yana da Ikirarin cewa wai Musulmai sun kasa amsa tambayoyinsa. Sai Imam Abu Hanifah ya matsa kusa dashi yace masa “In sha Allahu ni zan amsa tambayoyin naka komai wahalarsu”. Mutumin ya amsa gayyatar, Kuma Jama’a suka cika da mamaki. Ta yaya wannan ‘dan Qaramin yaro zai iya jayayya da Kafirin nan wanda manyan Maluma suka kasa ja dashi!

Da ranar Mukabalar tazo sai Jama’ar garin gaba daya suka taru a wani fili a tsakiyar garin Baghdad wanda dama anan ake gabatar da duk wani Muhimmin taro. Sai shi wannan kafirin ya hau kan tudun dake tsakiyar taro. Sannan ya bude muryarsa ya jefo tambayarsa ta farko zuwa ga Abu Hanifah; “Shin menene Allahn naku yake yi dai-dai yanzu? Abu Hanifah ya tsaya yayi tunani na ‘yan mintuna kadan, sai yace ma mutumin “To ina so kai ka sauko kasa, ni kuma in hau sama sannan in baka amsarka”. 

Wannan yaro karamin yaro ‘dan shekara goma (wato Imam Abu Hanifah) ya hau saman kan tudun sannan yace “Ya Allah kaine shaida gareni agaban duk wadannan Mutanen cewar na shaida lallai yanzun nan kai ka Qaddara saukowar wannan kafiri zuwa Qasa, kuma ka Qaddara cewar Mumini zai hau sama (wato zai daukaka akansa)”.

Da Mutane (‘yan kallo) suka ji wannan amsar ta fito cikin fasaha daga bakin Abu Hanifah, sai suka fara kabbara “Allahu Akbar!” Allahu Akbar!” Tun daga nan kafirin nan ya fara ganin kaskanci.
Amma sai ya sake jefowa tambayarsa ta biyu “Shin meke raye kafin Allahn naku?” (Subhanallah). Imam Abu Hanifah (rah) yayi tunani zuwa wani lokaci sai yace ma kafirin ya Qidaya masa lambobi daga goma zuwa Qasa Sai kafirin ya fara “Goma, tara, takwas, bakwai, shida, biyar, hudu, uku, biyu, daya, sufiri” Sai Imamu Abu Hanifa yace masa “Shin me ka gani bayan sufiri (wato zero)?”

Mutumin yace “Babu komai kafinsa, ni ban sani ba”. Da jin haka sai Imam yayi murmushi yace masa “To gashi nan ka riga ka bawa kanka amsa...Hakika Allah shine rayayye kuma dawwamamme. Babu kowa kuma babu komai kafinsa”. Daga wannan sai waje ya rude da kabbara, suna Qara jinjina ma Imam Abu Hanifah (rah). Kafirin nan zuciyarsa ta harzuka, ransa ya baci. Sai ya jefo tambayarsa ta Qarshe “SHIN YANZU WAJEN INA (WACCE KUSURWA) ALLAHN NAKU YAKE KALLO?” (Shin gabas yake kallo ko yamma ko kudu ko Arewa?). Imam Abu Hanifah bayan yayi tunani zuwa wani lokaci sai yace a kawo masa Fitila (Aci-balbal ko kuma kyandir). Da aka kawo masa sai ya damka wa kafirin nan. Yace masa ya kunna masa, Bayan kafirin ya kunna kyandir din sai ya tambayi Imam Abu Hanifa , to menene dalikin haka? Sai Imam Abu Hanifah yace masa “Shin wanne waje ne wutar hasken kyandir din nan take kallo?” Sai kafirin yace, “Tana kallon dukkan kuskuwoyi ne. (wato gabas, yamma, kudu, arewa, sama da Qasa) Babu inda bata kallo” Sai Imamu Abu Hanifa yace masa “Ai ka riga ka amsa tambayarka. Hakika Hasken Allah ya mamaye ko ina. Yana nan ako ina, babu wajen da babu shi”.

Daga nan sai mutane suka rude da kabbarori “Allahu Akbar! Allahu Akbar!! Allahu Akbar!!!”. Shi kansa wannan kafirin yayi mamakin ilimi da basirar Imamu Abu Hanifa (RA). Don haka anan wajen ya furta kalmar Shahada, ya zama Musulmi kuma ya zama Almajirin Imam Abu Hanifah (ra).

Imam Abu Hanifah yana daga cikin mutane mafiya kaifin hankali da basira daga cikin Maluman wannan al'ummar ta Musulunci. Watarana barayi sun shiga gidan wani mutum suka yashe masa dukiyarsa baki 'daya, sannan suka sanyashi ya rantse akan cewa ba zai tona musu asiri ba. Idan kuma ya tona asirinsu to Matarsa ta saku, Saki uku!! Wannan mutum ya wayi gari cikin tsananin bakin ciki. yana kallon mutanen nan suna ta sayar da kayansa da suka sato, amma bashi da damar yace komai, tunda ya riga ya rantse idan ya fallashesu to matarsa ta saku saki uku!! Saboda haka sai yaje ya gaya ma Imam Abu Hanifah halin da yake ciki. Sai yayi Murmushi yace masa "Na san hanyar da zamu bi, kayanka zai dawo ba tare da kace komai ba". Sai Imam Abu Hanifah yasa aka tara masa dukkan Limamai da ladanai na garin, sannan yace musu "Wannan mutumin anyi masa sata ne. amma shin kuna so dukkan kayansa ya dawo gareshi?". Suka ce "Eh". Sai yace to ina so ku tattaro min duk mutanen da aka ta'ba tuhumarsu da sata a unguwanninku.

Da aka tattarosu sai yasa aka kira masa Jami'an tsaro, yace musu ga wasu mutane nan zan rika tambayar wannan mutumin game dasu. Duk wanda kuka ji wannan mutumin yayi shuru bai ce komai akansa ba, to 'barawo ne. ku kamashi. Sai Imam Abu Hanifah yasa aka rika fitowa da mutanen nan 'daya bayan 'daya. Yana tambayar mutumin nan "SHIN WANNAN NE BARAWONKA?". Sai mutumin yace "A'a ba shi bane". Sai ace wannan ya wuce. Amma idan aka tambayeshi "SHIN WANNAN NE BARAWONKA? " in aka ji yayi shuru bai ce komai ba, sai Imam Abu yace "KU KAMA WANNAN SHIMA BARAWO NE".

Da haka sai da aka kama dukkan barayin nan ba tare da mai dukiyar ya ambaci sunayensu ba.
Allah Mai kyauta da karawa kamar Yadda Imamu Abu Hanifa Yake da kaifin basira haka Allah ya Azzurtashi da 'ya mai kaifin Basira. Abu Hanifa ya kasance yana karba tambayoyi tare da bada fatawowi hadi da karantarda dalibban Ilmi.

Wata Rana Sai aka yi masa wata tambaya wacce ta daure masa kai, tambayar kuwa itace; "ME YASA A MUSULUNCE SU MATA BA'A BASU DA DAMAR AUREN MAZA FIYE DA DAYA BA, ALHALI SU MAZA NA AUREN MACCE HAR UKKU?" Wannan tambayar ta daurewa Imam Abu Hanifa kai sosai da Sosai, Cen 'yarsa da ke Zaune Kusansa (wato Hanifa), Sai tace, "Ya Babana ai zan iya karba wannan tambaya Idan har ka amincemin."

Abu Hanifa Ya amince mata akan ta bada amsar wannan tambaya in har ta san amsa. Hanifa ta sa aka tara mata 4 ta bukaci a kawo katon masaki cike da nono, bayan an kawo wannan masaki, Sai tabawa kowace macce kofi daya tace kowacce ta debo wannan Nono dake cikin wannan Masaki. Bayan kowacen su ta debo (Wannan Nonon), Sai tace, dukansu su mayarda nonon a ciki. Dukansu suka sake mayarda nonon da suka diba. Sai Hanifa tace, "To kowaccen ku ta debo Nonon da ta zuba a cikin Wannan masaki, ba tare da ta debo wanda bata zuba ba."

Dukansu sai suka ce, "Taya zamu iya debo nonon da muka zuba kuwa? Alhali nonon ya hade?"
Sai Hanifa Tace, "To kamar hakane, Idan macce ta auri maza biyu ko ukku ko hudu, aka haihu ba za'a iya gano waye mahaifin jarinrin ba." Wannan Amsa ta Sanya Numan bin Thabit (Abu Hanifa) farin Ciki, daga nan sai aka rika kiransa da sunan (Baban Hanifa).

A shekarar 763, Imamu Abu Hanifa ya samu takardar Bukatar yayi Jagorancin alkalin Alkallai daga Al-Mansur a zamanin Kaliph Harun al-Rashid. Lokacin da Wannan takarda ta sami Abu Hanifa sai ya Rubutawa Al-Mansur Cewa, "Hakika ni Ban cencancan ci Zama kan wannan Mukamin ba abawa wani." Lokacin da Sako ya Zowa Sarki Al-Mansur sai ta yasa aka kira masa Imamu Abu Hanifa Yace Masa Me yasa ba zaka Amsa ba? Abu Hanifa Yace, Ban Cen-centa bane kawai.

Al-mansur Ransa ya bace Yace, "Hakika Karya Kake yi domin ka cen-centa." Sai Imamu Abu Hanifa Ya buda baki yace, "Babu Shakka bayani na ya tabbata (ban Cen-centa ba), taya zaka dauki Matsayi na Alkalin Alkalai Ka bawa makaryaci?" Wannan amsar ta Abu Hanifa Ita ta harzuka wannan Sarkin nan take ya sa aka kama Imamu Abu Hanifa aka Rufeshi a Gidan kaso (Prison) aka Rika azabantar dashi azaba kala-kala a gidan yarin. 

Duk da Irin Azabar da Imamu Abu Hanifah yake sha masana tarihi sun tabbatarda ci gaba kawai yayi da karantarwa da yin Kira zuwa a kadaita Allah a Cikin Wannan Gidan kaso. A karshe dai wasu malaman tarihi sun bayyana a gidan yarin Allah ya karbi ransa.
Masana tarihi suka ce kusan mutum dubu hamshin (50,000), ne suka halarci zana'Izarsa a lokacin da Allah Yayi Masa Cikawa.

Daga cikin littafan da ya wallafa akwai, Fiqh al-Akbar; Fiqh al-Abasat Kitaab-ul-Aathaar, Kitabul Aathaar, Musnad Imaam ul A'zam, da kuma Kitaabul Rad alal Qaadiriyah. Imam Abu Hanifa ya hardace hadisai masu yawan gaske har an ruwaito wani daga cikin magabata na cewa, Imamu Abu Hanifah ba ya rawaito hadisi sai wanda ya haddace, ba ya rawaito hadisin da be haddace ba. Imam Abu Hanifa ya rasu a shekarata (150A.H).

Jamilu Sani Rarah Sokoto
Mon 17-04-2017

Saturday, 22 April 2017

GUDUMMUWAR MAWAKAN HAUSA A CIKIN AL-UMMA

GUDUMMUWAR MAWAKAN HAUSA A CIKIN AL-UMMA
******
Sau tari Wasun mu sukan Rik'ajin haushi tare da Sukar mawaka musamman namu na Hausa tare da yi musu kallo a matsayin 'yan Iska ko kuma masu b'ata tarbiyar Al-ummah. Hak'ik'a kafin In kawo gudummuwar da suke bayarwa yana da kyau in yi bayanin wata aya a cikin al-qur'ani wacce wasu da yawa basu san dalilin Saukar taba, amma daga zarar Sunji anyi maganar mawaki sai su kawo ayar a matsayin Hujjar Qin wak'a. Ayar da take Cikin Suratush-Shu'ara'I aya ta 224 In da Allah (Swt) Yake Cewa; "WASH-SHU'ARA'U YATBA'UHUMUL-GH AAWUUN" Ma'ana "Kuma mawaƙa halakakku ne ke bin su." (Sura shu'ara'i aya ta 224).

Ibn Jareer da Ibnu Abi-Haatim sun fitar da hadisin daga Babban Malami Masani tafsirin al-qur'ani wato Ibnu Abbas cewar; Wasu mutane (mawaqa) su biyu sunyi ma juna habaici (alokacin Manzon Allah (Saww), Daya daga cikinsu mutumin madina ne. Dayan kuma ba d'an madina bane. Sun kasance a koda yaushe sukan soki junansu da munanan kalamai a waken da suke, kuma kowannensu yana da masu binsa suna zuga shi daga cikin danginsa.

Sai Allah (Swt) Ya Saukar da fadinSa Cewa, "Kuma mawaƙa halakakku ne ke bin su." To wayancen dangin nasu sune Allah yake nufi da "Halakakku" (su da ke zugi domin ayi zage-zage).
Har wayau Imamul-hakim da Ibnu Jareer sun karbo hadisi daga Abu Hasan Albarrad cewar: "bayan da wannan ayar ta sauka wash-shu'ara'u. Sai Wasu daga cikin mawakan Annabi (Saww), Irinsu Abdullahi Ibn Rawaha da Ka'abu Ibn Malik da kuma Hassanu Ibn Thabit (rta) suka je wajen Manzon Allah (saww) suka ce: "Ya Rasulil Lahi Gashi Wannan aya ta Sauka, Kuma Allah yasan Cewar, Mu mawaka ne. Shikenan mun halaka." Nan da nan sai Allah (Swt) ya sake Saukarda wata ayar Inda Allah (swt) yayi istisna'i garesu cewar. "ILLAL-LADHEENA AMANU" ma'ana "Sai dai wadanda sukayi imani kuma suka aikata ayyuka na kwarai kuma suka yi zikirin Allah da yawa" (Shura'I aya ta 227). Sai Manzon Allah (Saww) ya kirawo su ya gaya musu tare da karanta musu Ayar domin hankalinsu ya kwanta.

Mai Neman karin bayani ya duba, Usudul-ghaabah- Juzu'i na 3 shafi na 235. Tirmidhy ma ya fitar da hadisin ta isnadi mai Qarfi, a duba a Sunanut-Tirmiziy hadisi mai lamba 2851 da kuma SIYARU A'ALAMIN-NUBALA 'I juzu'i na 1 shafi 236 domin karin bayani. Nasan wani zaice to ai Wakokin Hausawa babu komai a cikin su in ban da sakarci da sharholiya da kuma son a kwaikwayi Indiyawa, Babu shakka duk mai irin wannan tunani zan iya kiran shi wanda bai waye ba ko kuma ma bai da zurfin tunani domin wakokin Hausa suna taka muhimmiyar gudummawa ga addinin musulunchi da ma al'umma a kebe.

Muna sane da cewa kafin finafinan Hausa su samu babu finafinan da suka fi na Indiyawa karbuwa a kasar Hausa, kuma idan an duba za a ga akwai wakokinsu wadanda babu komai a ciki face yabon gumakansu da sauran abubuwan bautarsu, to ire-iren wadannan wakoki ne mutanenmu suke yi da bakinsu, ba su san mene ne ma’anar abubuwan da suke fada ba, amma wakokin da ake yi a finafinan Hausa kowa ya san abin da ake fada, sannan ana ambaton Ubangiji da Annabinsa da kuma yabo gare su, kafin a shiga gundarin wakar ko a tsakiyarta ko kuma a karshenta (Wanda ake kira Introduction and Conclusion a turance). Wannan ba karamar gudumuwa bace domin da yanzu Allah kadai ya san wanda ya hardace wakokin bautar gunka. Mu Janye maganar Gudumuwa wak'a na da tasiri a wajen jan hankalin al'umma daga cikin mawakan a zamanin Annabi (Saww) akwai Hassanu bin Thabit (rta) kamar yanda na ambata a baya, Babu shakka Annabi (Saww) da kansa ya tab'a umurtarsa da ya tashi ya mayarwa da wasu mawaka da suka ci mutunchin Annabi (Saww) da martani.

Bayan wancen K'arnin Bincike ya nuna cewa, mutum na farko wanda ya fara rubuta littafi a kan ilimin ma'aunin waka wanda da Larabci ake kira Arudhi shi ne Khalil Ibn Ahmad Alfarahidi Albasari, a karni na biyu. Marubucin ya rasu a shekara ta 174 bayan hijira Annabi Mahamadu (Saww) wacce ta zo daidai da shekarar ta 791 Shekarar alak'ak'ai Miladiya. To, amma kuma tarihi ya nuna cewa, kafin shi wannan bawan Allah ya rubuta wannan littafi akwai mawaka da suke rubuta wakoki, ko da ya zo ya rubuta wannan littafi sai ya dace da ma'aunin ire-iren wakokin da suke yi tun dauri. Dalilin da ya sa ya rubuta wannan littafi shi ne, Khalil ya yi kwadayin ilmi irin na Sibawaihi wani malamin Nahawu ko kuma marubucin Nahawu, sai ya fita yana kewaya Ka'aba yana rokon Allah ya ba shi baiwa ta ilmi, sai Allah ya yi masa baiwa ta wallafa littafin ilmin ma'aunin waka, Arudhi. A cikin littafin ne ya takaita waka a kan ma'auni goma sha shida. To, amma da yake rubutun nawa ba yana magana a kan ilimin wakar ba ne, bari na mayar da alkalami na a saman hanya, wato kar ya yi ratse.

Amma ya yakamata a yi wakar? Kasancewa a al'adar bahaushe tana tafiyane tare da addinin musulunce, to kamata yayi idan za'a yi wakar ta kasance namiji ne kadai ke rairata banda macce, haka idan macce za'a nuna tana wakar to kada a hada ta da namiji. Misali, akwai wani fim mai suna Wani Gari. A fim din ai ba'a hada mata da maza suna rawa ba, kawai an nuna jarumin ne shi kadai yana karanta wakar. Haka a fim din Salma shima jarumin ne kawai ke waka banda macce, haka fim din Jiddah shima macce ce kadai ke wakar ba tare da namiji ba. haka ya kamata wakokin finafinan Hausa su kasance domin kare mutuncin al'adar mu da kuma addinin mu.

Babu shakka ina goyon bayan Wakoki da finafinan Hausa sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba nuna saurayi da budurwa suna waka da rawa a tare wannan sam ba al'adar Hausawa ba ce sam domin duk wanda ya kalli irin wa dannan wakoki a finafinan Hausa zai ga abin sam ba tsari. sai da me kuma? masu kallo ne ke sanya ana sanya saurayi da budurwa a tare domin su a ganinsu idan ba haka akayi ba sam ba'a burgesu ba. saura Gudumuwar fina-finan Hausa.

Jamilu Sani Rarah Sokoto
Sat 22-04-2017

Friday, 21 April 2017

DALILAN DA KE NUNA SAMUWAR ALLAH (SWT), ZUWA GA ATHEIST.

DALILAN DA KE NUNA SAMUWAR ALLAH (SWT), ZUWA GA ATHEIST.
*****
Zuwa ga Masu da'awar Cewa, Babu UBANGIJI (Swt), Atheist a turance ku sani Duniyar nan gaba d'ayanta tana mai tabbatarwa da shaidawa da fad'in cewa, akwai Allah Mai girma da buwaya.

A cikin Al-qur'ani Mai Girma Allah Madaukakin Sarki yana cewa,“Manzanninsu suka ce, yanzu akwai shakka a cikin samuwar Allah, wanda ya halicci sammai da qassai, yana kiranku don ya gafarta muku zunubanku ya jinkirta musu zuwa wani lokaci sananne. Sai suka ce, kufa ba kowa ba face
mutane kamar mu, kuna so ne ku kange mu daga abin da iyayenmu suke bautawa, ku zo mana da wata hujja mabayyaniya” (Suratul Ibarahim aya ta 10).

Hakika Mumini shi ke da yaqinin cewa, Allah Madaukakin Sarki shi ne Ubangiji, mai iko, ya kuma tabbatar da cewa shi ne abin bautawa shi kadai. Ta yaya zaku tsaya akan neman dalili akan samuwar abin da shi ne dalilin samuwar komai da kowa? Idan muka haura zuwa ga dalilan da suke nuna samuwar Allah, za mu samu dalilai masu yawa kamar haka:

DALILIN SAMUWAR ALLAH NA FIQRA: Babu wani abu da za ka yabi Allah da shi face da falalarsa da ni’imominsa, a kowane hali kana buqatar Allah mai girma da buwaya. Asalin halitta an yi ta ne a kan imani da Allah mahalicci. Babu wanda yake barin wannan abin da aka halicce shi a kai na imani da Allah mahalicci sai wanda Allah ya rufewa zuciya da hankali.

Daga cikin manya-manyan dalilai da suke nuna an halicci mutum a kan imani da samuwar Allah Mad'aukakin Sarki Shine, fad'in Manzon Allah (Saww) cewa, “Dukkan wanda ake haihuwa ana
haihuwarsa akan asalin halitta, iyayensa ne suka mayar da shi bayahude ko banasare ko ba majuse, kamar irin yadda dabba take haihuwa, shin kuna ganin ana haihuwar dabba mai yankakken kunne?” (Imamu Bukhari ne ya rawaito sh).

Dukkan wani abin halitta ya yarda da kadaita Allah a yanayin halittarsa Allah (Swt) ya ce, “Ka tsayar da fuskarka a kan addini, kana mai karkata ga barin qarya.Halittar Allah ce da ya halicci mutane a kanta, babu canji ga halittar Allah. Wannan shi ne addini miqaqqe sai dai da yawan mutane ba su sani ba” (Suratur rum aya ta 30). Wad'annan dalilai na hankali suna nuna samuwar Allah mad'aukakin Sarki.

Sai tabbatuwar da samuwar Allah a hankalce ya fi kowane dalili qarfi ga duk wani wanda shaidanu ba su janye shi ba, a cikin Al-qur'ani mai girma Allah Mad'aukakin Sarki yana cewa, “Halittar Allah ta asali da ya halicci mutane a kanta” (Suratur rum aya ta 30). Bayan ya ce “Ka tsayar da fuskarka ga addini kana kaucewa barna”. (rum : 30).

Sunan Allah suna ne da aka zana shi a cikin halittar kowa, ba ya buqatar wani dalili fiye da wannan.
Lafiyayyen hankali yana shaida wa da samuwar Allah, amma wanda shaidanu suka janye shi zai iya qin wannan dalili ya ji ba ya buqatarsa. Amma idan ya fada cikin wata matsala babba, sai ka ga hannayensa da idanuwansa da zuciyarsa sun nufi sama kai tsaya suna neman taimako da agaji daga Ubangijinsa. Domin ya koma halittarsa ta asali madaidaiciya.

DALILIN SAMUWAR ALLAH NA HANKALI: Daga cikin manya-manyan dalilai masu qarfi, wadanda ba wanda zai yi musu akansu sai mai jayayyar runto kadai, akan tabbatar da samuwar Allah mahalicci, daga cikinsu akwai

1-Dukkan halitta akwai wanda ya halicceta: dukkan wad'annan ababen halitta gaba d'ayansu akwai wanda ya samar da su, domin ba zai yi wu su samar da kansu da kansu ba, saboda babu
abin da ya halicci kansa, don kuwa babu shi kafin samuwarsa, to kuma ta yaya zai samar da kansa, don dukkan wani abu samamme akwai wanda ya samar da shi.

Sannan kuma samuwar wadannan abubuwa akan wannan tsari mai kyau, hadadde, mai tafiya tare da sababi, a hade da juna, ba zai yiwu ba a ce haka kurum abun ya faru kwatsam, a’a dukkan wani mahaluki ba makawa yana da wanda ya halicce shi. To idan kuwa abin haka yake, to lallai Allah ne Ubangijin talikai ya samar da su, Allah Mad'aukakin Sarki ya fad'i wannan dalili inda yake cewa “Shin an halicce su ne daga babu, ko kuwa su ne masu yin halittar?” (Suratud Dur aya ta 35).

Allah yana nufin su ba haka kurum akan halicce su ba, ba tare da wani wanda ya halicce su ba, kuma ba su suka halicci kawunansu ba, to dole suna da wanda ya halicce su, wanda shi ne Allah Madaukakin Sarki.
Don haka ma a lokacin da Sayyidina Jubairu d'an Mud’im (RA) ya ji Manzon Allah (Saww) yana karanta suratud Duri, ya zo kan wadannan ayoyi, inda Allah yake cewa, “Shin an halicce su ne daga babu, ko kuwa su ne masu yin halittar. Ko su ne suka halicci Sammai da Qasa, a’a ba su yi yaqini ba. Ko a wajensu akwai taskokin Ubangijinka, kai ko su ne wadanda suka mamaye komai” (Suratud Dur aya 35 zuwa 37).
A lokacin Jubairu yana mushiriki bai musulunta ba, amma duk da haka sai ya ce, “Zuciyata ta kusa ta tsinke na musulunta” (Bukhari ne ya rawaito shi).

Dan adam tare da dimbin ilimin sanin duniya da Allah ya ba shi, har yanzu ya kasa gano wasu abubuwa na boye wadanda babu abin zai kawo qarshen cece-kuce a kansu sai kawai imani da akwai Allah shi kadai.
2-Bayyanannu ayoyin Allah a cikin duniya da halittarsa. Allah Madaukakin Sarki ya ce, “Ku duba (ku yi tunani) mene ne a cikin Sammai da Qasa” (Yunus : 101).

Saboda a cikin duba sammai da qasa zai bayyana Allah ne mai halitta, kuma ya qara tabbatar da
kadaituwar Allah da ayyukansa. An cewa wani mutumin qauye, dame ka gane Ubangijinka? Sai
ya ce, “Alamar sawu tana nuna tafiya, kashin raqumi yana nuna akwai raqumin. To yanzu sama
mai matakalai, da qasa mai hanyoyi, da teku mai igiyar ruwa da yawa, yanzu wadannan ba za su
nuna akwai Allah mai ji mai gani ba?”.

3-Tsaruwa lamarin duniya da kyautatuwarsa, dalili ne akan wanda yake tsara shi, shi ne abin
bauta shi kadai, kuma mamallakinsa shi kadai, Ubangiji shi kadai, babu wani abin bauta sai shi, kamar yadda ba zai yi wu ba a samu Ubangiji biyu, masu halitta kuma wadanda suka yi daidai da juna, to haka ma ba zai yiwu a samu ababen bauta guda biyu ba, waxanda suka yi daidai da juna.

Kuma ba zai yi wu a samu wadanda suka yi duniya su biyu ba, abu ne tabbatacce a hankali, to haka ma ba za a samu abbaben bautawa guda biyu ba.

DALILIN SAMUWAR ALLA NA SHARI'A: Dukkan Shari’u suna nuna samuwar wanda ya yi halitta, kuma suna nuna cikar iliminsa da hikimarsa da jinqansa, saboda dukkan shari’u ba makawa da wanda ya shar’anta su, wanda shi ne Allah Mai girma da buwaya, Allah (Swt) yana cewa, “Ya ku mutane ku bautawa Ubangijinku wanda ya halicce ku, da wadanda suke gabaninku ko kwa samu taqawa. Wanda ya sanya muku qasa ta zama shimfida gareku, ya sanya kuma sama ta zama gini gareku, ya saukar daruwa daga
girgije, ya fitar da ‘ya’yan itace arziqi gareku, to kada ku sanya wa Allah abokan tarayya alhali kuna sane” (baqra aya ta 21 zuwa 22).

DALILIN SAMUWAR ALLAH NA JI DA GANI: Daga bayanannun dalilai da suke nuna samuwar Allah Mahalicci akwai dalilin da duk mai hankali yake gani kuma yake jinsa, kamar:

1-Amsa addu’o’i: Mutum yana roqon Allah, ya ce, “Ya Ubangiji” ya roqi wani abu, sai kuma ya ga an amsa masa, to wannan dalili ne da ake gani dake nuna samuwar Allah Ubangiji, saboda Allah ya amsa masa, kuma mutum ya ga hakan quru-quru.

Haka ma muma sau da yawa mun ji misalai a da, da yanzu na cewa Allah ya amsa musu abin da suka roqa. To wannan wani lamari ne da yake nuna samuwar Allah Mahalicci, a cikin Alqur’ani akwai dalilai irin wadannan da yawa, daga cikinsu akwai fad'in Allah, “Ka tuna (Annabi) Ayyuba lokacin da ya kira Ubangijinsa cewa cuta ta shafe ni, Allah kuma kai ne mafi jinqai masu jinqai. Sai muka amsa masa” (Al’anbiya aya ta 83 zuwa 84). Da ayoyi da yawa irin wad'annan. Kore samuwar Allah cuta ce a cikin hankali, kuma matsala ce a cikin tunani.

2-Shiryar da halittu zuwa ga abin da yake shi ne sirrin rayuwarta. Wanene ya shiryar da mutum zuwa ga kama mama yayi da aka haife shi? Wanene ya shiryar da Al-Hudu-Hudu har yake gane wurin ruwa a qarqashin qasa, wanda ba wanda yake ganin hakan sai shi? Haqiqa Wannan aikin Allah ne, yana cewa: “Ubangijinmu wanda ya halicci dukkan komai kuma ya shiryar da shi” (Daha aya ta 50).

3-Ayoyin da Allah ya aiko Annabawa da Manzanni da su, su ne Mu’ujizozin da Allah ya qarfafa su da su, ya zabe su, daga cikin mutane ya fifita su. Dukkan wani Annabi Allah ya aiko shi da wata mu’ujiza zuwa ga mutanensa, tana tabbatar da cewa abin da aka aiko shi da shi daga wajen Allah ne, mahalicci abin bauta shi kadai, babu wani abin bauta wanda ba shi ba.

Sannan har wayau daga Cikin dalilai na hankali da ke nuna Samuwar Allah (Swt), akwai yin Arziki ko talauci, babu shakka duk wanda zai ce babu Allah to yana Fadar son ransa ne. Domin idan ka duba a kusa da kai a kwai mai kuddi ko Ilmi wanda kake burin Inama ace kai ne, makawar kuwa kai ka halicci kanka to zaka Mayarda kanka kamar wancen da kake muradin zama kamarsa.

Abinda Zan Cewa, Masu da'awar Babu Allah d'aya ne Zuwa Biyu, Na farko Ina yi musu murna da Suka Shaidi Cewa, Babu Allah. Dalili kuwa Yana daga Cikin Sharuddan Karbar Addinin Musulunchi wato La'Ilaha (ma'ana "Babu Wani abin Bauta") don haka ina jan hankalinsu tun lokaci bai kire ba Su karbi ragowar ILLALLAH (ma'ana "Sai Allah").

Ina Fatan Duk wanda Ya Samu Karanta wannan Rubutun Zai taimaka da Share domin Wayannan mutanen suna nan Suna ta Jan yan Uwanmu a cikin wannan muguwar Ak'ida ta BABU ALLAH.

Jamilu Sani Rarah Sokoto
Thu 20-04-2017

KUYI HANKALI DA 'YAN DAMFARA

KUYI HANKALI DA 'YAN DAMFARA
******

A Ranar 07 ga watan Mayun Shekarar 2014 Jaridar Khaleej Times ta k'asar Dubai ta Ruwaito Labarin Wata Makekiyar damfara da aka yiwa Wata Mata 'yar k'asar Dubai Dirham miliyan hudu, wanda ya yi daidai da Naira miliyan 160 a kuddin Nageriya.

An damfari wannan matar ne don a cire wa ’yarta aljanin da ya hana ta aure. Jaridar ta Ruwaito Cewa, Al’amarin ya samo asali ne a lokacin da matar ta shiga damuwa, ganin cewa tsararrakin ’yarta sun yi aure, amma ita 'yarta ko labari babu. Da ta shiga tunanin yadda za ta aurar da ’yarta, sai kawar yarinyar ta nuna mata cewa akwai wata amtsala a cikin al’amarin ’yarta, inda ta nuna mata cewa aljani ne ya aure ta. Ita kuwa jin haka, sai ta yarda. Daga nan sai aka nuna mata cewa za a samo mata maganin aljanin da ya hana ’yarta aure.

Bayan kwanaki kadan, sai aka bayyana mata cewa aljanin da ya auri ’yarta yana da tsananin kishi, don haka ba zai kyale kowa ya aure ta ba. Kuma shi yake korar duk wanda ya nuna yana son ’yarta.
An dai cusa wa matar ra’ayin ta tuntubi wata bokanya, wadda ta bukaci ta ba Dirhami miliyan guda wato daidai da Naira miliyan 40. Wannan bokanya, sai ta kara da cewa abin wuyanta ma aljani ya kama shi. Don haka aka ce ta bayar da abin wuyan, wanda kimarsa ta kai Dirham dubu 700.

Bayan da ta aikata abubuwan da aka bukaci ta yi, sai kuma bokanya ta bukaci ta biya wasu dirhami miliyan biyu da dubu 700, don gudanar da wannan gagarumin aiki na cire aljani. “Wanda Jimlar kudin da bokanya ta bukaci a biyata sun kai Dirhami miliyan hudu (Naira miliyan 160),”.

Jaridar ta Khaleej Times, ta ruwaito cewa, wannan mata ta yi yunkurin sayar da gidanta, don haka ta bayar da cikon kudi na tsawon lokaci, inda za a dauki shekaru har zuwa 20 tana biyan kudin. Sai kawai aka aiko mata da sammaci, wai ana binta bashi.

Ganin haka, sai ita ’yarta suka kai kara gaban hukuma, aka kuma bincika, aka gano cewa, matar da ta yi musu wannan kulle-kullen an sha kama ta da laifin damfara. Hukumar Shari’a ta birnin Abu Dhabi ta bayar da cikakken rahoton damfarar, inda ta bayyana cewa,tuni matar ta bukaci hukuma ta dakatar da biyan wannan ciken kudin, a kuma soke amfani da shi kacokam.

Wannan Labarin Ya dade da faruwa, amma dalilin da ya sa na kawo shi shine, yanzu wasu mayaudara sun fara yawo a cikin wannan k'asa ta nigeriya da sunan bada magani. Yanda suke yi Shine, Idan suka zo a Unguwa Zasu tambaya Waye mai kuddi sosai a wannan Unguwar? Idan aka nuna musu sai su tambayi sunan 'yarsa Ko matarsa. Idan aka gaya musu sai su samu farar Leda su cika ta da Iska makil suyi Tsibbace-Tsibbacensu Da sunan matar ko 'yar Mutumen.

Nan take Ita kuma wacce aka yi wa wannan Asiri abin zai kama ta Sai cikinta ya Cika kamar Zai fashe, tare da Jin Matsanancin Jiri. Za'ayi ta neman magani amma ba za'a dace Ba, kuma su wayannan macuta sukan Sicce Wannan Cikin yau gobe kuma su Sake Hura shi.

Bayan Sati d'aya ko biyu zasu bayyana a Gidan da sunan Su masu bada magani ne zasu taimaka, A haka zasu kawo magani su bayar tare da Sanya miliyoyin kuddin da za'a bayar Idan ta samu sauki. Bayan kwana biyu sai suje su Sacce wannan ledar marar lafiyar ta dawo kamar bata tab'a ciwon ba. Wannan fa Shine damfarar da ake yi a yanzu.

Ina Mafita? Idan Irin Wannan Ya Faru a Unguwarku Ga Wata Mafita Da Ta tabbata daga Sunnar Manzon Allah (Saww). Za'a samu Fitsarin Rakumi da Nononsa a Rik'a bata tana sha In shaa Allahu Allah zai Cubutar da mai lalurar daga Makircin Wayannan Masihirta.

An Samo hadisi daga Manzon Allah (Saww) yace, Ku nemi nonon rakumi yana maganin duk wata cuta da ke cikin ciki. Haka Kuma An karbo daga Annabi (Saww) Yace: Nonon rakumi da fitsarin rakumi suna maganin cutar dake cikin ciki wadda ake kira (Dharibah).

Har Wayau Jaridar Emirati mai lamba 11172 wacce ta fito a shekarar fabairu 2006 ta rubuta wani bincike da tayi akan Rakumi inda ta kawo cewa abu mafi amfani da yake jikin Rakumi akwai nononsa yana tasiri wajen maganin ciwon zuciya da narkar da abinci da cututtuka da suka shafi daji da sauran cutuka.
A wani bincike da Dr Ahlam al-awadi yayi wanda magazine na al-da'awa suka buga mai lamba 1938 a shekarar 2004 ya ce, akwai amfani mai yawa a cikin nonon Rakumi daga cikin abinda ya kawo ya tabbatar da cewa fitsarin Rakumi na yana taimakwa wajen maganin cutar da ta shafi fata yana gyra ga shi ya sanya shi kyalli da laushi ya kuma fidda amosarin kai. Haka Kuma Fitsarin Rakumi Yana Maganin Kambun Baka da Sihiri Da Iznin Allah. Abin Lura Dai wannan ya faru da Wasu 'yan Uwa kuma Mashaa Allahu an samu waraka.

Note: Dharibah wata cuta ce dake cikin ciki, idan anci abinci baya narkewa har sai ya rube. To idan an sha nonon rakumi bayan an gama cin abinci, yana gusar da
wannan matsalar.
Wannan Damfarar Tuni na dade da Sanin ta Sai dai Yanzu abin ya fara Yawaita don Haka a Kula Jama'ah.

Jamilu Sani Rarah Sokoto
Thu 20-04-2017

Monday, 30 January 2017

SHAHARARREN DAN FASHI IGNAC GOLDZIHER

SHAHARARREN DAN FASHI IGNAC GOLDZIHER
******
Goldziher Na daga cikin wayanda suka kware wajen farautar Imanin Musulmi ko kuma rudarda kwakwalwar Musulmi, (Orientalist).

Goldziher shahararren Malamine masani a kowane fanni na Addini musulunchi.

An haifi Goldziher a wani garin da ake kira Szekesfehervar na yahudawa a cen yayi rayuwarsa yayi karatunsa a university of Budapest, da kuma University of Berlin dake Germany.

Ya shiga aikin gwamnati a Germany inda ya rika matsayin ministan Al'aduna Germany.

Daga nan sai ya tafi kasar Syria, domin karatun addinin musulunchi, daga Syria sai ya wuce Egypt, domin ya koyi ibadodi a wajen wasu malamai

Goldziher ya rika zuwa masallatai wurin malamai masu wa'azi a masallatai a cikin cairo, in da yayi ta daukar karatu a wajensu.

Goldziher ya rika rubuta duk abinda ya gani ko yaji tare da hardace wasu daga cikin Wakokin Hikima na Larabawa. Lokacin da ya koma Jamus sai ya rika wallafa karyaryaki game da musulunchi a kasar ta Jamus.

Goldziher ya bayyanawa kiristoci cewa, "Hakika idan kuna son Ku samu galaba ga musulmi, to babu shakka sai kun Fitarda matayensu daga cikin gidaje sun rika fita neman abinci."

A lokacinda suka yi wannan zama Sai Zuweimar (daya daga cikin 'yan fashin Imani) Ya bayyana Cewa, "Hakika idan muka juyar da musulmi muka mayardasu addinin kirista mun yi musu gata, abinda ya kamata muyi shine, Mu barsu da sunan musulunchin amma kuma babu ruwansu da addinin."

Goldziher yana daga cikin Wayanda sukayi ta juyarda musulmi daga Musulunchi da sunan kira suke zuwa musulunchi.

Hakika akwai irinsu Goldziher har a yanzu kuma sunanan suna rubuce-rubuce da Hausa da turanci a facebook da Whatsapp don haka yana da kyau 'yan Uwa mu kula.

Jamilu Sani Rarah Sokoto
Mon 30-01-2017

Sunday, 8 January 2017

MARVIN GAYE TSINANNEN MAWAKI

MARVIN GAYE FITSARARREN MAWAK'I
*********
Marvin Gaye Marubucin Wak'ok'in Turanchi ne kuma ya Shahara a fannin wak'ok'i. Shahararsa musammance domin duk kamfaninsu mai suna "Motown record company" babu kamarsa.

Marvin Gaye yayi kuriciyarsa a garin Washington, D.C, In da anan ne ya girma kuma anan ya koyi wak'ok'insa.

Mahaifin Marvin Gaye Sunansa Marvin Gay, Sr, kuma shahararren Pasto ne a Washington, D.C, sunan mahaifiyarsa kuwa Alberta Gay.

Marvin yakoyi wakok'i a Cocin mahaifinsa (Inda mahaifinsa ke yiwa arna Wa'azi), Marvin ya shiga aikin soja a lokacin da yake d'an Shekara goma sha bakwai (17 years). Da haihuwa.

Marvin gaye ya daina aikin Soja a Shekarar 1962 yaci gaba da Wak'ok'insa Inda har ya samu yin fice a harkar wakar.

Bayanai duk sun tabbata cewa Marvin Gaye da Mahaifinsa basu da Jituwa kusan kowa haushin wani yake ji tun Marvin Gaye na yaro k'arami. A Lokacin da yana k'arami akan Kira shi da Marvin "Gay" ne.

Bayan d'aukakarsa ta fara fitowa fili sai Marvin Gaye ya fara zazzakar sunan mahaifin nasa “Gay”, daga nan ne ya k'ara harafin ‘E’ a k'arshen Sunan "Gaye" maimakon "Gay" domin nesanta kansa daga sunan mahaifinsa.

A 1 ga watan Aprilun shekarae 1984, Marvin gaye suka samu sab'ani shi da mahaifinsa har ya harbe shi da bindiga har lahira a gidansu dake Los Angeles.

Abinda ya faru kuwa shine Mahaifinsa yazo ya same shi kwance tare da mahaifiyarsa Alberta Gay kwance a saman gado d'aya kuma ba tufa a jikin Marvin gaye.

Kafin Wannan kamawa da mahaifinsa yayi masa da akwai wata wak'a da yayi wacce ya sanyawa "Sexual Healing".

Daga Cikin wannan wakar akwai Inda Marvin Gaye ke Cewa;

"Sexual healing, baby, it's good for me Sexual healing is something that's good for me"

"Well, it's good for me and it's so good to me my baby, ohh Come take control, just grab a hold
Of my body and mind, soon we'll be making it, honey I'll be feeling fine,

"You're my medicine, open up and let me in Darling, you're so great, I can't wait for you to operate."

"I can't wait for you to operate When I get this feeling I need sexual healing Oh when I get this feeling
I need sexual healing I gotta have sexual healing, darling 'Cause I'm all alone Sexual healing, darling
Till you come back home Please don't procrastinate It's not good to masturbate"

Ma'ana;

"Warakar Jima'I nake Nema 'Yan Mata, Saboda tafi dacewa dani, Waraka daga jima'I tana matukar dacewa dani"

"Hakika Tafi dacewa dani, Saboda haka yana da kyau kizo ki kwance tufana ki Rik'e dukkan Jikina da Zuciyata, bada b'ata lokaci ba zamu samu biyan buk'ata, Ya zuman Zuciyata hak'ik'a idan mukayi haka zan samu waraka"

You're my medicine, open up and let me in Darling, you're so great, I can't wait for you to operate

"Kece Maganina, don haka ki bud'emin In shiga abar sona, kina da babban matsayi, da ba zan iya jure kici gaba da aiki ba."

Ba zan iya jure kici gaba da aiki ba a duk lokacin da na tsinci kaina cikin wannan yanayi. Hakika idan na samu kai na a cikin wannan hali nakan nemi waraka ta hanyar yin Jima'I, don haka sai na nemi waraka ta hanyar yin Jima'I, ya abar sona sai ke dawo gida kuma kada ki jinkirta dawowa ke san biyan bukata da Hannu baida kyau"

Wannan Wak'ar Marvin ya Rubuta tane a lokacin da Bashi da lafiya (yana kwance a gida), ashe mahaifiyarsa yake yiwa Ita.

Lokacin da Marvin Ke yin wannan wak'ar Mahaifinsa yayi Yayi ya daina yinta domin kada ya zubar masa da mutunchi a matsayinsa na Babban Malamin Arna.

Abinda Shi Wannan Mahaifin Be sani ba shine, Marvin Mahaifiyarsa ce yake son Yayi lalata da Ita.

To a lokacin da ya gansu a kwance saman gado tare sai ya dauko bindiga ya yi masa harbi biyu (wasu kuma suka ce Ukku), a kirji aka kaishi asibiti a cen Ya rasu.

Bayan Mahaifin Nasa Ya Marvin Ya gasu shi kuma mahaihinsa aka yanke masa hukuncin kisa (Saboda kisan da yayiwa d'ansa).

Binciken Likitoci Ya nuna Marvin da Mahaifinsa dukansu mashaya Hodar Iblis ne da Barasa.

Kuma Likitocin Sun tabbatar da Cewa, Shan Giya da Hodar Iblis (cocine) ne suka sanya masa Sha'awar Mahaifiyarsa.

An tab'a tambayar Wata 'yar Uwar Mavin Gaye ko meyasa Tsana tsakaninsa da mahaifinsu Sai tace, mahaifinsu ya dad'e yana kokwanto akan cewa, shin Marvin d'ansa ne ko kuma d'an Wani.

Jamilu Sani Rarah Sokoto
Sat 07-01-2017