Tuesday, 12 November 2019

MAGANAR MAULUDI ABUNE MAI SAUKI

Dukkan dangin Yabo da godiya da kirari su kara tabbata ga Allah (Swt), Salati da Sallama su kara zuwa ga Shugaban Annabawa Fiyayyen dukkan Halittu Muhammad 'dan Abdullahi (Saww).

Bayan haka Wannan rubutu zai haska ma akan Halaccin yin Mauludi ko kuma haramcin Yinsa a mahanga ta addini.

Farko hakika a cikin Qur'ani mai girma babu wuri daya In da Allah (Swt) yayi umurni da ayi Mauludi

Annabi (Saww) da kansa baiyi Mauludi ba kuma bai Umurci wani daga cikin Sahabbansa Suyi Mauludi ba.

Sai dai ma Annabi (Saww) ya Umurci Sahabbansa da kada su yi koyi da Nasara Domin Sune ke yin Biki domin Annabi Isa (Alaihis Salam).

Yace, "Kada ku rike ni kamar Yadda Nasara suka riki d'an Maryam. Ni bawa ne. Saboda haka kuce dani Bawan Allah kuma Manzon Allah (Saww)." (Buhari).

Ya tabbata Manzon Allah (Saww) ya kan dauki ranar haihuwarsa Ranar Ibada ba ranar Biki ba kamar yanda yazo a hadisi.

An Tambaye shi (Saww) game da Azumin Litanin da yake yi, sai yace, itace Ranar da aka haifeni kuma itace ranar da aka bijiromin da alkawali (Muslim, al-Nisaa’i da kuma Abu Dawood).

Baya ga haka mun san Cewa, Sahabbai (RA) sun fimu So da Kaunar Annabi (Saww).

Sayyidina Abubakar (RA) Wanda Yafi kowa kusanci ga Annabi (Saww) ba'a samu yayi Mauludi ba.

Ko An samo a littafan Tarihi Cewa, Sayyidina Umar (RA) yayi Mauludi ko Sayyidina Usman ko Aliyu (RA)?

Ko an samu daga Cikin 'ya'yan Annabi (Saww) Wani yayi Mauludi? Shin basu san da mauludin bane ko kuma Son Annabi (Saww) ne basayi?

Bayan Sahabbai Shin Imam Abu Haneefah, Maalik, Shaafi’i, Ahmad, al-Hasan al-Basri, Ibn Seereen an samu Waninsu yayi Mauludi?

An samo a hadisi Ingantacce daga Ma'aiki (Saww) Cewa, Annabi (Saww) yace, Mafifitan mutane daga cikin Al'ummata sune Karni Na Farko (Sahabbai Kenan), Sannan masu bi musu (tabi'ai Kenan), Sannan Masu bi musu (Tabi'ut tabi'una Kenan)" (Bukhari, Muslim Da Tirmiziy Suka Ruwaito).

Idan Zamuyi duba Kenan Wannan Karni Namu Yana Kasa Kwarai game da Samun fifiko kamar yadda Annabi (Saww) Ya Fada.

Shin Ba Akan soyayya bace ake yin mauludin ba? Shin munfi Sahabbai Soyayyar Annabi (Saww) NE? Domin kuwa daga Cikin Sahabbai akwai Wanda Manzon Allah (saww) ya kwanta barci akan cinyarsa lokacin da suke cikin wani Kogo.. Sai Shi wannan sahabin ya rika yagar rigarsa yana tottoshe ramukan da suke cikin kogon. Amma duk da haka akwai sauran wani rami wanda bai samu abin tosheshi ba.

Chan sai ga wani Maciji ya leko ta cikin wannan ramin yana so zai fito. Don haka sai ya sanya Qafarsa ya toshe ramin don kar Macijin nan ya fito ya chutar da Manzon Allah (saww). Macijin nan yayi ta cizonsa yana zuba masa dafi. Amma duk da haka bai motsa ba, don kar ya tashi Manzon Allah (saww) daga Bacci. Wannan Sahabi Shine Sayyidina Abubakar.

Shine Makusancin Manzon Allah (Saww) na Kusa da Kusa Kai akwai ma Lokacin da Manzon Allah (saww) yazo gidan Sayyiduna Abubakr (ra) yace masa “ALLAH YA UMURCENI INYI HIJIRA”.

Sai Sayyiduna Abubakar yace “Ina fatan tare dani zaka tafi?” Sai Ma’aiki yace masa “KWARAI KUWA. ALLAH YACE MIN IN TAFI TARE DAKAI”. Sai Sayyiduna Abubakar ya fashe da kuka don murna Ganin Allah ya zabe shi ya Raka Wanda Yafi so a Duniya Fiye da Komai.

Kai Hatta Annabi (Saww) An tambayeka Shi Duk Duniya Waka Fi so Yace, Aisha, Aka sake Tambayar say Cikin Maza fa? Yace, "Mahaifinta (Wato Abubakar)".

Amma Duk Irin Wannan Soyayyah dake Tsakanin Sayyidina Abubakar da Manzon Allah Bai sa Sayyidina Abubakar Yayi Mauludi Don tunawa Da Annabi (Saww) ba.

Bayan Sayyidina Abubakar (rt), Sayyidina Umar (ra) na daya daga cikin zaratan mayaka wadanda su kayi ruwa da tsaki wajen kare martabar Musulunci da ruguza abokan fadansa.

Ya kusanci Manzon Allah (Saww) har ya kai matsayin wazirinsa na biyu. Bayan tsabar Soyayyar da Sahabi Umar Ke yiwa Annabi haka Allah ya karrama shi da surukuta da Manzon Allah (Saww) inda Manzon Allah ya nemi auren 'yarsa Hafsah, aka ba shi ita, aka daura aure, sai ta zama ita ce ta uku. Bayan Sayyidina Abubakar Yayi wafati Sayyidina Umar NE Yayi khalifanci Amma Baiyi Mauludi ba Bai Kuma yi Umurni da ayi Mauludi ba.

Sayyidina Usmanu Bayan zamansa Sahabi a gun Annabi (Saww) Kuma surukine na Annbi (Saww) domin ya auri 'Ya'yan Manzon Allah har Guda biyu Amma ba'a Taba samunsa ba dayi Mauludi ba.

Haka Dan baffansa Sayyidina Aliyu tun Yana karaminsa Ya Yarda da abinda Annabi (Saww) Yazo dashi, domin tun Yana Dan Shekara Bakwai ko Tara ya karbi Musulunchi Kuma surukin Annabi (Saww), Wanda ya auri Daya daga Cikin 'ya'yan Annabi (Saww) (Kusan ma Wacce Annabi Yafi so a Cikin 'ya'yansa).

Sayyidina Aliyu Shine, Wanda ya yarda ya amince ya kwanta akan Shimfidar Ma’aiki (saww) acikin daren da Mushrikai suke nufin su kasheshi (Saww).

Sayyidina Aliyu ya yarda ya kwanta amadadinsa, duk da yasan cewa zasu iya harbinsa da kibiya ko su kasheshi tun kafin su gane cewa ba Ma’aikin bane awajen. (saww), Amma Duk da Irin wanna So Annabi Ya yo wafati ya barshi Duniya baiyi Mauludiba Bai Kuma yi Umurni da ayi mauludin ba.

Sayyidina Bilal Shine Ladanin Manzon Allah (Saww) bayan Ma'aiki (Saww) Ya bar Duniya Saboda Tsananin soyayyarsa ga Ma'aiki (Saww) Sayyidina Bilal dena kiran sallah yayi!!

Bilalu (rta) bai Qara yin kiran sallah ba Sai rannan Sayyiduna Umar (ra) yace masa yazo yayi (aranar da aka karbo Masallacin Qudus).

Da Bilalu ya fara kiran sallah, yazo daidai wajen “ASH-HADU ANNA MUHAMMADAR RASULULLAH!! Yana fada haka, sai ya fashe da kuka, Sahabbai ma kowa sai kuka.

An ce ba’a ta’ba ganin ranar da daruruwan Sahabbai sukayi kuka suka zubar da hawayesosai kamar wannan ranar ba.. Sai sukaji Tamkar awannan lokacin ne Ma’aiki ya bar duniya!! Amma Duk da Wannan Basuyi Mauludi ba.

Imamu Malik Saboda Soyayyarsa ga Ma'aiki (Saww), Baya Fadin hadisi a Hanya, Idan Ka tambayeshi hadisi a hanya sa Yake a dake Ka, Idan zai Bayyana hadisi sai Yayi wanka ya Sanya Turare Saboda Tsananin Soyayyarsa ga Fiyayyen Halitta (Saww).

Har an Ruwaito Cewa, Baya hawan Doki a Madina, Baya saka takalma a Madina Da aka tbayeshi dalili Yace, Saboda Baya it's takin Kasarda Annabi (Saww) Yake a Ciki, Amma Duk da Irin Wannan Soyayyah da Yake yiwa Annabi (Saww) ba'a Samu Yayi Mauludi ba.

Shin kana tunanin duk sun Manta NE da Ranar haihuwar Annabi (Saww)? Ko Kuma basa son shine? Ko Kuma Tunaninsu da fahimtarsu Bata Kai Cen ba?

'yan Uwana Masu Murnar Mauludi Kuyi Hakuri Dolene sai Mun Tunatarda kanmu abinda Yake daidai ko zamu Samu Rabo a Gobe Qiyama.

Muna Rokon Allah ya nuna Mana Gaskiya Kuma ya Bamu Ikon Binta, Ya Kuma Nuna Mana Karya Ya Kuma Bamu Ikon Kauce Mata.

Jamilu Sani Rarah Sokoto
Tue 12-11-2019