Sunday, 7 April 2019

SUWA KE BADA KWANGILA DOMIN TABA DARAJAR SARKIN MUSULMI

Masu iya Magana sunce, Kowace Magana da lokacinta, haka kuma Kowane Lokaci da maganar da ta dace dashi, akan haka naga dacewar inyi irin wannan rubutu a wannan lokaci domin kowama (wanda ya sani da wanda bai sani ba duka) su san cewa, Jemage Ba Tsuntsu bane, Domin da yawa zaka samu wasu daga cikin mutane na kallon jemage a matsayin tsuntsu Alhali kuwa ba tsuntsu bane.
Wannan Rubutu zanyi shine zuwa ga kalar mutane guda biyu, Na farko sune, Wayanda ke karbar kwangila domin shiga kafafen yada labarai domin wargaza hadinkan Al’ummar musulmi. Mutane na biyu kuma masu bayarda kwangilar (daga baya kuma su fito suce ba su sukace ayi ba). To duk muna sane da ku da kulle kullenku na wargaza hadin kan musulmi da Allah (Swt) ya umurcemu da yi, domin hadin kai Allah ne ya kwadaitarda yinsa a tsakanin Al’umma. Haka kuma zagin Shugaban Musulmi (Wanda ke da Ikon fadar anga wata ko ba’a gani ba shima wargaje zaman lafiya ne), Idan zaka dubi Alqur’ani gaba daya zaka tarar yana karantarda hadin kai tare da biyayya ga shuwagabanni.

Misali, a cikin suratul Fatiha Allah (Swt) Yana cewa, “Ihdinas-Siraat-Al-Mustaqeem” (Ma’ana, Ya Allah ka shiryar damu ga hanya madaidaiciya), To meyasa Idan zakazo wajen karanta wannan ayar ta Ihdinas-Siraat-Al-Mustaqeem meyasa baka ce, Ihdinis-Siraat-Al-Mustaqeem ba (Ma’ana Ya Allah ka shiryarda ni ga hanya madaidaiciya) Saboda a nuna mana muhimmacin hadin kai.

Haka kuma a wajen fadin “Iyyaka na'aboudou wa iyyaka nasta'in” (Kai muke bauta kuma kai muke neman taimakonka) Meyasa bakace, ” Iyyaka a'aboudou wa iyyaka asta'in” (Kai nake bauta kuma kai nake neman taimakonka) ba? Ubangiji (SWT) Ya sanya wannan ne domin ya kara nuna mana muhimmanchin hadin kai. Babu shakka Idan kaje yin sallah ko kai kadaine (kuma ko a ina ne dole lamirin mutane na biye da kai) domin a nuna maka muhimmanchin hadin kai.

Bayan wannan ma Saboda Ubangiji ya kara nuna mana muhimmancin zaman lafiya ya sanya mana Sallah biyar a wuni, Sallar ma ba’a amince ka rufe daki kai kadai kayi ba in banda Uzuri, dole sai ka fito a masallachin Unguwa kayi sallar, Wannan kai tsaye kowa ma yana iya fahimtar karatun cewa, ana so a nuna mana hadin kai ne.

Haka a duk sati zamu hadu kusan yan Unguwanni da yawa muyi sallar jumu’ah wannan ma hadin kai ne ake nuna mana, Kai k ace wannan bai Isa ba Ubangiji ya sake sanya mana Wasu salloli biyu a shekara domin kawai a Kara nuna mana muhimmanchin hadin kai.

Duk dai domin Ubangiji ya nuna mana Muhimmanchi tare da Soyuwarsa akan mu hada kai, Ubangiji ya sanya mana Haduwa a saman dutse guda kwaya daya tal (Dutsin Arfa) tare da sanya Lada mai tsoka ga duk wanda ya samu damar halartar wannan tsayuwa a wannan dutse (na Arfa), Da zaka je ka samu Tsauni a garinku ko kasarku kaje a wannan rana kayi tsaye da zummar kayi tsayuwar arfa to wannan tsayuwar batayi ba, ba saboda komai ba sai don Allah (SWT) Ya nuna mana muhimmanchin hadin kai (Musamman na Musulmi).

Akan haka ne ma Allah (SWT) Yayi shuwagabanni (Annabawa) kuma yace a bi bayansu kuma yayi shuwagabanni na Al’umma ya kuma bada umurnin abisu a wurare daban-daban,

Misali, Idan Kuka zo zakuyi Sallah Dole ne ku sanya dayanku a matsayin liman kuma dole ne duk abinda yayi shi zakuyi a matsayinsa na shugaba a wajenku a wajen sallah. Bayan ya fara karatun fatiha duk zakuyi shiru kuna saurarensa, Bayan y agama yace, Amin Sannan kuma kuce. Wannan kai tsaye yana nuni da yin biyayya ga Shugaba (Akan abinda yake halat).

Amma yau Saboda lalaci na neman duniya wasu bata gari wayanda basu son ganin musulunchi yaci gaba suna so su kawo suka ga wayannan shuwagabanni. (Ya Allah ka shiryesu), Bazan Manta ba a Shekarar da ta gabata Shiekh Ahmad Gummi Yaje wajen Shirya Atiku da Obasanjo Nan da nan gari ya kaurace ana zaginsa tare da tsinuwa wanda kuma sam Abokan zaman mu ba haka suke ba.

Misali a wannan tafiyar da Shiekh Ahmad Gummi yayi yaje wajen wannan shiri a tare da shi akwai shugaban Kiristoci Rev. Hassan Maku Kuka wanda har yaje ya dawo baka ji Kiristan ko daya ba daya gaya masa Magana marar dadi. Wannan kai tsaye zai nuna mana kura kuran da mukeyi. Na yarda da wasu bata garin Mutane suna Amfani damu domin mu rika batanci ga shuwagabannin mu.

Ina wannan rubutun ne Ya’Allah Allah yasa su masu bada kwangilar suji tsoron Allah su daina, domin babu shakka Mun sansu kuma Idan muma muka ari Jahilcinsu muka fara bazasuji dadinmu ba ko kadan, Domin muna nasane da ko suwaye masu bada kwangilar (Akwai Mai Gida Yamma akwai Mai Gida Gabas) don haka Larabawa suna KARIN MAGANA Cewa, “MAN ANZARAKA FAQAD A’A ZARAKA” (Ma’ana Wanda ya Gargadeka Hakika ya gama shiryarda kai).

Jamilu Sani Rarah Sokoto
Mataimaki na Musamman ga Sarkin Musulmi akan Sababbin kafofin yada labarai
Sun 07/04/2019