MUTUWAR AURE A KASAR HAUSA INA MAFITA?
Allah (SWT) da kansa ya kira 'ya macce da sunan Nutsuwa a gun mazaje, duk ilmi, kuddi ko Sunan da 'da namiji yayi bazai taba samun nutsuwa ba sai tare da 'ya mace.
Shi yasa Allah da kansa a wani wuri a cikin Alqur'ani ya kirayi 'ya'ya mata da lafazin Sutura a gun maza ba don komai ba domin anuna mana muhimmanci da kimar 'ya'ya mata a gidan duniya. Domin duk kuddinka ko Ilmin ka ba zaka iya tafiya tsirara ba.
To amma wani abin ban haushi a yanzu zaka tarar mazajen yanzu basa kula da wannan qima da martabar da Allah (Swt) Ya baiwa 'ya'ya mata. Wani babban abin haushi da ke faruwa a wannan kasa tamu, musamman a wannan bangaren namu na Hausa Fulani.
Tun ina Qidayawa har na gaji da kirgawa na zubawa sarautar Allah ido tare da addu'ar Allah ya kawo sauki game da wannan matsalar
Ko kunsan me nake kirgawa? Kananan 'Yan mata wayanda ake yawan saki ba tare da sun mayar da shekara da yin aure ba. Wannan abu ba karamin 'daga min hankali yake ba.
Wallahi nasan kusan macce 5 zuwa 6, 7 da suka fito daga gidan mijinsu ba tare da sun mayar da shekara a gidan na aurensu ba. Kuma galibi duk zaka same su yara 'yan kanana wayanda shekarunsu ba zasu haura 23 zuwa da 24 ba.
Duk lokacinda aka sanya muhawara akan me yake kawo sakin aure a kasar Hausa zakayi tajin bayanai daban-daban. Wasu zaka ji sunce rashin ladabin 'ya macce ne, Wasu kuma zaka ji sun ce rashin tsafta da kula da mai gida ne, Wasu kuma zaka ji sun dauki laifin gaba daya sun daura shi akan namiji suce rashin hakuri ne.
A iya bincike da nazarin da nayi game da mace-macen Aure da ke faruwa a yanzu na gano wasu daga cikin wayannan dalilai da ke sanya saurin rabuwa a tsakanin ma'aurata.
Da farko akwai rashin sanin ma'anar aure da kuma raahin sanin darajar da ke cikin aure, galibi maza da matanmu duka muna suna yin aure ne ba don zamansa ibada ba. A'a suna yine saboda dakushe sha'awar da ke damunsu. To da zarar akayi aure wannan sha'awar ta kau ko kuwa sai kowa yaji ya gaji da 'dan uwansa. Domin dama ita sha'awa kamar wutar karace saurin cenyewa take.
Abu na biyu kuma akwai rashin bin ka'idojin da musulunci ya sanya wajen yin aure. Yana daga cikin abinda Manzon Allah (Saww) ya karantar da musulmai Ya ce, Ku zabar wa 'ya'yanku uwa tagari.
Ta yaya zamu zabarwa 'ya'yanmu Uwa ta gari? Anan ma Annabi (Saww) bai barmu a kara zube ba sai da ya gaya mana yanda zamu zabe ta. Yana daga cikin hanyoyin zaben mata tagari yin istihara (addu’a ce manzon Allah (Saww) ya koyar da al’umarsa. Duk wanda ya tashi neman aure ya yi istihara.Ita wannan sallar raka’a biyu ake yi sannan a karanta addu’ar).
A addininmu musulunchi ba'a yarda mutum ya fara nemman aure ba, ba tare da ya yi istikara ba. Bayan ya yi istihara sai kuma ya shawarci mutanen kirki da wadanda suka santa.
Domin mace ita ce uwa ta farko ga ‘ya’yanka. Yara suna tasowa ne a kan dabi'unta da halayenta. Haka a addinance ba'a a lura da kyawon mace wajen aure, domin ba shi ne mazon Allah (Saww) ya ce a lura da shi ba.
Manzon Allah (Saww) ya ba da
labari yake cewa, Ana auren mata saboda abu hudu (4): Wasu suna auren mace saboda dukiyarta, wasu kuma suna auren mace
saboda kyawonta, wasu kuma suna auren mace saboda danginta, wasu kuma suna auren mace saboda addininta. Sai Annabi (Saww) ya ce na horeka da ka aure ma’abociya addini.
A Wani hadisin da ibn Maajah ya ruwaito Manzon Allah (Saww) ya ce, “Kada ku auri mata saboda kyawon su, kyawonsu yana iya
juyar da ita.( ta kasance mai girman kai.) Sai ya qara da cewa, “Kada ku auri mata saboda dukiyarsu: Ana sa ran dukiyarsu ta sanya su girman kai. Sai dai ku aure su saboda addini.
Wani mutumi ya je majalisin Safiyanu bn Uyaynah ya ce, “Ya Aba Muhammad ina fama da matata tana wulaqanta ni matuqar wukaqantawa. Sai Safiyanu bn Uyaynah ya yi shiru kadan sannan ya ce, “Me yiwuwa ka aure ta ne saboda ka samu daukaka.” Sai mutumin ya ce, “Lallai haka ne. Sai ya ce, “Duk wanda ya auri mace saboda neman daukaka, to Allah zai qasqantar da shi. Wanda kuma ya auri mace saboda dukiya Allah
zai jarabce shi da talauci. Wanda ya auri mace saboda addini to Allah zai hada masa daukaka da dukiya da addini.
Kunga kenan wannan duk yana nuna mana kada muyi aure don sha'awar macce tana fara ko tana da kyawo ko 'yar gidan masu kuddi ce da sauransu. A'a anan ana so ka dauki aure a matsayim ibada kuma ka auri macce ba dan komai ba sai don addininta
Ko kun san muhimmancin auren macce mai addini? Idan baku sani ba ku tsaya kuji. Imamu Shafi’i babansa ya rasu tun yana dan jariri amma da yake uwarsa mai addini ne a wajenta ya haddace Qur’ani mai girma.
Imam Ahmad bn Hambal ya ce shekaransa talatin da matarsa amma bata taba saba masa ba ko jayayya da shi bata taba yi da shi ba, Amfanin mai addini ke ne kenan.
Babu shakka rashin auren macce mai addini yana daga cikin manyan dalilan da suke kawo mutuwar aure a wannan zamani da muke ciki.
Don haka yana da kyau maza a ji tsoron Allah a rika yin Aure don Allah ba don Sha'awa ko daular gidansu yarinya ba yana da kyau a rika daukar aure a matsayin bauta babu shakka wannan zai rage mace-macen auren da ke faruwa a zamanin nan.
In shaa Allahu zan dakata anan a gaba zan kawo siffofin macce mai addini da kuma irin Suma mata mazan da ya kamata su aura da kuma yanda za'a rika walwale husuma da zarar ta faru tun ba'a kai ga saki ba. Dan uwanku a Musulunchi Jamilu Sani Rarah Sokoto Nigeria.
In da nayi dai-dai Allah ka bamu lada mu duka In da nayi Kuskure ba daga ni bane daga Shaidanne Allah ka yafe mana.