Daga cikin Malaman Da Shehu Usmanu Danfodiyo ya Tarar a
Wannan Kasa Akwai Muhammad Alamin Alkanemi (Wanda yake Zaune a Borno yana
Sarauta) Shi wannan Malamin Mahaifinsa Balarabe ne daga gari da ake kira
Fazzana (dake cen Cikin Croatia).
Kamar Yadda Tarihi yazo Cewa, Wannan Malamin Kafin Zuwan
Shehu yaje Makkah domin yin aikin hajji daga cen kuma sai ya wuce garin
Mahaifinsa Fazzana domin ya ziyarci dangin Mahaifinsa daga baya kuma sai ya
dawo kasarsa borno.
Kasancewar Tafiya a wancen lokacin tana da wuya, (domin mutum
yakan shekara da shekaru bai samu yaje garin da zaije ba), wannan yasa Bayan
dawowarsa sai ya tarar da Daawar Shehu ta mamaye ko Ina a fadin wannan kasa ko
kuma Daula a wancen lokaci. Inda Shehu da Almajiransa suka yi waazi suka
shiryarda mutane zuwa ga hanyar gaskiya, wayanda kuma suka ki jin wa’azi Shehu
ya yakesu (A cikin wayanda aka yaka kuwa harda Jama’are da Hadeja) da sauran
wasu garuruwa wayanda suke cikin Rikon
Borno.
Wannan dalili shiyasa Muhammad Alamin Alkanemi Ya zargi
jihadin Shehu Usmanu Bin Fodio Inda ya nuna Jahdin na Shehu bai dace ba (Ma’ana
bai dace ya yaki wasu garuruwa ba), a cikin wayannan garuruwa da bai dace a yaka
ba akwai mutanen da Borno ke riko, Dominsu Mutanen Borno da wayanda suke riko
Musulmi ne.
Wannan daliline ya sanya Alkanemi ya rubuta wasika Ga Shehu
yana zargin Jahadinsa, Bayan Wasikar Alkanemi ta zowa Shehu da Almajiransa, nan
take Shehu ya Umurci da Muhammad Bello Dansa da ya mayarwa da Alkanemi amsar
wasikarsa.
A haka Alkanemi ya rika turo wasika inda shi kuma Shehu yana
sanya Bello yana maida martani. A Wannan yanayine Allah (Swt) ya karbi ran
Shehu Usmanu (Allah ya jikansa da Rahama), Har bayan Mutuwar Shehu Aminu
Alkanemi bai daina turo wasika bag a Sarakunan Daular Usmaniya, Inda daga
karshe dai Alkanemi ya Rubutowa da Muhammad Bello wasika akan Cewa, Zaizo ya
yaki Daular Usmaniyya. Kuma zai fara yakar Kano (tunda tana daga rikon Daular
Usmaniyya dake da Hedkwata a Sokoto).
Bayan Samun wasikar Alkanemi Sai Sarkin Musulmi Muhammad
Bello ya rubutawa da Yakubun Bauchi (Sarkin Bauchi), Akan Cewa, Ya tari
Alkanami da yaki (Wanda a lokacin (Kai harma a yanzu ) Sarkin Bauchi yana
karbar Umurni ne daga Sarkin Musulmi dake Sokoto).
Inda nan take Yakubun Bauchi ya shirya Rundunar yaki yaje ya
tari Aminu Alkanami (Suka gwabza yaki mai yawa a tsakaninsu), daga karshe
Yakubun Bauchi ya samu nasara ga Alkanami, Nan take Alkaname ya gudu, Shi kuma
Yakubun Bauchi ya bishi har tsawon kwana ukku bai kama shi ba.
Wannan Dalili yasa aka Bawa YAKUBUN BAUCHI (SARKIN YAKIN
YAKIN SARKIN MUSULMI MUHAMMADU BELLO), Wanda har yanzu Jikokinsa (Wayanda suke
rike da Sarautar Bauchi suke, Rike da Sarautar Sarkin Yaki).
Don haka duk mai tunanin Ayi masa Sarautar Sarkin Yakin
Sokoto to yanama daina wahalar da kansa domin Sarauta ce mai tarihi ba Sarauta
ce ta Cuwa-cuwa ba.
Jamilu Sani Rarah Sokoto
Mon 04-03-3019
Mon 04-03-3019