AMFANI DA KANYA A MATSAYIN MAGANI
BOKANCINE
********
Kwanannan Naje Qauye domin ziyara
sai na taradda wani al'amari mai ban takaici wanda kusan tun daga wannan rana
kullum sai na rika tunani akan wannan al'amari.
Al'amarin shine Wani audio ne ake
yawo dashi, wanda wani Mutum ke bayanin Abubuwan da zasu faru a wannan shekara,
Inda yace, An aiko shine Daga Saudiya, Kuma duka-duka su Ukku kawai aka aiko a
duniya, sannan yace, Wannan shekarar bala’o’I da yawa zasu faru ma’ana shekara ce
ta BALA’I, Sannan wannan mutumen yaci gaba da cewa, Duk wanda yasan yana yin
bacci tun daga dare har safiya ta waye, to ya daina Idan bai daina ba to kuwa
zai mutu matsiyaci a wannan duniya.
Wannan Mutumen ya fadi abubuwa da
yawa wanda lokaci ba zai iya barni na kawo suba, Daga karshe dai ya bada magani,
Inda yace, A nemi Kanya tana maganin cutukka da yawa a ciki kuwa hard a Ciwon
HIV inda yayi rantsuwa cewa, Idan bata maganin HIV Allah Ubangiji yasa HIV ya
zama ajalinsa (Iyazan Billahi Iyazah).
Farko dai Wannan Mutumen yayiwa Allah (swt) Qarya, Domin Cewa da yayi
wannan shekara ta bala’ice to yana karyata fadin Allah (swt) ne a cikin Alqur’ani
Mai girma.
Domin Al-Imamul Bukhaari ya ruwaito hadisi daga Saalim bn Abdullahi, bn
Umar, daga Baban Saalim din, wato ( Abdullahi dan Umar(RA)), Yace, Manzon Allah
(Saww) yace: “Mabudan Gaibu guda 5 ne, kuma babu wanda yasansu sai Allah (Swt). Sune Allah ya dunqule su a qarshen
Suratu Luqman, inda yace: “Lallai ILIMIN TASHIN QIYAAMAH yana wajen Allah ne,
kuma shike SAUKAR DA RUWAN SAMA, kuma YASAN ABINDA KE CIKIN MAHAIFA, kuma RAI
BATASAN ME ZATA SAMUBA GOBE, KUMA WATA RAI BATASAN A WACE QASACE ZATA MACE BA,
lallai Allah masanine mai bada labara” – Imamu Bukhari ya ruwaito a hadithi na
4627, a babin tafsiri.
Kenan Cewa, da wannan mutum yayi, Bala’I zai faru a wayannan shekaru
kamar yana cewa ne yasan abinda zai faru gobe (Wa’iyazubillahi), Kai tsaye
zamuce wannan mutum ya karyata Allah da ManzonSa (Saww). Allah ya kyauta.
Cikin bayanan Wannan mutumen yayi Rantsuwa tafi a Kirya, Wanda wannan
Ma fasikancine. Domin a cikin Rantsuwowin da malamai suka karkasa to kuwa yayi
babba daga cikinsu.
Wannan rantsuwa itace, Al-Yaminul-Ghamus ((Rantsuwa mai halakarwa), Wannan Rantsuwa malamai suka ce, ita ce:
Rantsuwar da mutum zai yi ta akan karya domin cin hakkin wani. Saboda irin
girman da wannan rantsuwar take da shi Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su
tabba a gare shi ya ke cewa "Dukkan wanda ya yanki hakkin wani mutum
musulmi da rantsuwar shi to hakika Allah ya wajabta mishi wuta kuma ya haramta
mishi Aljanna" Muslim ya ruwaito shi, (A’uzubillahi min zalik).
Sannan dukkan wanda ya bi wannan mutumen ya yarda da zancensa shima ya
sabawa Allah (SWT) domin Allah yana cewa
"Kada ka bi dukkan mai yawan rantsuwa, wulakantacce." Suratul-Kalam,
aya ta 10).
Abu na gaba ko na karshe da zamfadi da ke nuna wannan mutumen bokane
shine, KANYA ba ta daga cikin itacen da aka fada a cikin Al’qur’ani mai girma
da Hadisan Ma’aiki (Saww), Ku lura bawai ina cewa tunda bata cikin Alqur’ani da
Hadisai ba ba ina nufin bata magani bane A’a bahaka nake nufi ba
Shi wannan mutumen ya fadi cewa, KANYA ita kadaice Itacen da ta dade a
duniya domin tun rowan Duhana Ma’ana zamanin Annabin Farkon Annabi Nuhu (Alaihis
Salam) take, Itace kai bata mutu ba.
Kai tsaye Wannan Karyane domin Kuwa, tunda babu shi a Alqur’ani da
Hadisi to A ina ya samo haka? Ni dai nasan Jerin Itacen da suka zo a alqur’ani
da Hadisai In ganttatu In shaaa Allahu zan samu Lokaci In kawo su kamar yadda
Imamu IBN Khathir ya tattarosu a cikin littafinsa.
Abu na biyu da ke nuna wannan Mutum Boka ne shine, Yace, Ba’a dibar
wannan Itace sai Ranar LITANIN (monday), to meye matsalar sauran ranakkun? Babu
shakka wannan ire-iren sharuddan da Aljannu ke gin da yawa mutane masu huldayya
dasu ne don haka muyi hattara.
Idan mutum ya ci gaba da amfani da Ire-iren wayannan Sharudda babu
shakka ya Janyo ALJANNU su rika hulta da shine babu kakkautawa. Allah ya tsare
mu. Don haka mu kula.
Please A turawa ‘yan Uwa domin Suyi HATTARA Domin Amfani da Ita Aikin
Bokayene.
Jamilu Sani Rarah Sokoto
Sat 23/12/2017