Wednesday, 12 October 2016

ME YA FARU A RANAR 10 GA WATAN AL-MUHARRAM.

ME YA FARU A RANAR 10 GA WATAN AL-MUHARRAM.
*******
A Rana mai kamar ta yau ne, Ranar Goma Ga Watan Al-Muharram aka Kashe Jikan Annabi (Saww) wato Sayyidin Husaini (Rta). Sayyidina Husaini (Rta) An haife shi shekara daya bayan haihuwar wansa wato Sayyidina Hassan (rta), Dukansu suna da kama da Manzon Allah (Saww) daga cibiya har ya zuwa qasa. Annabi (Saww) ne ya sanya masa suna Hussaini.

Sayyidina Husain ya yi shada a ranar 10 ga watan Muharram a Karbala. Sakamakon rikici da ya faru a lokacin Mulkin Yazidu dan Sayyidina Mu'awiya. Sayyidina Husaini da Abdullahi bin Zubayr dukansu basu yarda da jagorancin Yazidu dan Mu'awiya ba. Dalilin Kin yardarsu da Mulkin kuwa lokacin da Sayyidina Mu'awiya (rta) yake kan Shugabanci, Sai ya bar Wasiyar Cewa, idan har Allah ya karbi ransa a bawa 'dansa Yazidu mulki.

Wannan dalili shiyasa Sayyidina Husaini Jikan Manzon Allah (saww) da Abdullahi bin Zubayr Jikan Sayyidina Abubakar (rta) suka ki amincewa da mulkin Yazidu. Saboda a ka'idar Mulkin musulunci a wancen zamani ba zaka ce a idan ka mutu a bawa danka ba sai dai su musulmi su zabi mutane masu daraja suyi musu kuri'ah duk wanda Allah ya bawa shikenan.

 Bayan Wannan abu ya faru Sai Sayyidina Husaini (rta) ya bar Madina ya koma makka da zama shi da Abdullahi bin Zubayr. Bayan An kashe Abdullahi bin Zubayr a Makka Sai ‘yan Shia daga kufa suka aiko masa wasika akan ya zo za su yi mashi mubaya’a. Sai Sayyidina Husaini (rta) ya tura 'dan uwansa Muslim ibn Aqeel akan yaje Kufa ya dubo masa shi wayannan wasikun da gaske ne ko kuwa karya ne.

 Daga nan sai Muslim ibn Aqeel yaje Kufa suka yi masa tarba ta arziki suka nuna masa ai da gaske ne su zasu taimaki Sayyidina Husaini (rta), nan take Muslim ibn Aqeel ya turawa da Sayyidina Husaini da Wasika akan yazo babu shakka da gaske suke akan zasu yi masa mubaya'a.

Da ya zo sai ya gane yaudaran sa suka yi, bai ga kowa ba sai rundinar UbaidulLahi ibn Ziyad.
A ranar 9 gawatan Muharram sayyidina Hussaini ya ce wa jama’arsa gobe akwai yaqi tsakani na da gwabnan Kufa duk mai son komawa gida ya bi dare ya tafi.

Rundunar gwabnan Kufa su 4000 shi ko sayyidina Hussaini ‘yan rakiyarsa 72, gari na waye wa sai yaqi ya barke, aka fafata aka fafutuka sahabi Hussaini ya nuna barde ne domin ya kashe jama’a masu yawa kafin yayi shahada. Ana cikin Wannan yakin ne Wani 'dan Shi'a mai suna Zur’atut Tamimi ya fara saransa a kafada daga nan sai Sinanu dan Annas wanda shima 'dan Shi'a ne ya soke shi da mashi a maqogwaronsa ya kuma qara cakansa da mashin a qirginsa.

kafin Sahabi Hussaini ya kai qasa sai Khuli al-Asbahi (La'anannen Allah) ya sa takobi ya sare kan sahabi Hussaini.(Ya Allah kar ka kai rahama ga wadannan mutanan da suka kashe sahabi Hussaini Ya Allah ka tabbatar da la’antarKa ga wadan da suka kashe Hussaini). Kafin a kashe sahabi Hussaini
ya nuna jarunta matuqa. Wannan yaqin ya faru ne bayan mutuwar sahabi Muawiyya da shekara biyu shi kuma Yazidu dan Sayyidina Muawiyya yana Sham. Bayan sun sare kansa sai suka Dauki kan sayyidina Hussaini suka tafi da shi Sham daga baya aka kai kan Sayyidina Hussaini a Madina aka rufe shi bayan kusan sati da faruwan yaqin. Ya Allah ka qara aminci ga jikan Annabinka ya Allah Ka qara daukaka darajansa amin.

'Yan Shi'a sun dauki ranar goma ga watan Muharram rana ce ta baqin ciki saboda a wannan ranar
ce a ka kashe jikan Annabi (Saww) a yaqin Karbala, wato Sayidna Hussaini (rta) wanda kuma Alhali sune suka kashe-shi da kansu. In da zaka kara gano 'yan Shi'a Munafukaine a Ranar ta goma ga watan Al-Muharram din da aka kashe Sayyidina Husaini hakama qannansa Abubakar da Umar da Usaman dukkan su ‘ya ‘ya ne ga sayyidina Aliyu (rta).

Amma abin ban mamaki ‘Yan Shi’a basa baqin ciki sauran yaran, sai Sayyidina Hussaini (rta) kawai
Allah sarki wannan zai ka qara fahitar damu cewa tsakanin sayyidina Aliyu (rta) da sauranan sahabai duk daya ne, tun da ga shi har yasa sunanayen sahabai Abubakar da Umar da Usman kuma tarihi ya tabbatar da cewa su ‘yan Shia da kansu su ka kashe Sayyidina Hussain A duba a littafin Shi’a Muntahal A’amal1 Shafi na 450 da I’ilamul wara na dabaris Shafi na 203 da Maqtalu Hussain shafi na 147 da Ma’alimi Madaratina shafi na 62 da kitabul Raudha dukkanin wadannan littafan na masu bi addini Shia ne da kansu su ka fada cewa 'Yan Shia ne su kashe Hussain bayan sun aika ma sa da wasiqu ya zo suyi masa mubaya’a, amma kuma suke baqin ciki na yaudara.

 Haka kuma Za'a iya Dubawa a Cikin Littafen Imamu Zahabi Mai Suna Siyar A'alamun Nubla. Sai mutum ya duba tarihin Sayyidina Aliyu, Dana Mu'awiya dana Sayyidina Husaini In shaa Allahu zaka fahimci makircin Shi'ah.

Jamilu Sani Rarah Sokoto.
Wed 12/10/2016